Masarautar Saudiyya ta biya yaran dan jaridar da aka kashe makudan kudade – Rahoto

Masarautar Saudiyya ta biya yaran dan jaridar da aka kashe makudan kudade – Rahoto

Yaran dan jaridar Saudiyya da aka kashe, Jamal Khashoggi, sun samu gidaje na miliyoyin dala sannan hukumomin masarautar na biyansu dubban daloli a kowani wata, jaridar The Washington Post ta ruwaito a ranar Litinin.

Wasu mutane 15 da aka aika daga Riyadh ne suka kashe Kashoshoggi wanda ya kasance dan adawar gwamnatin Saudiyya, a watan Oktoba a ofishin jakadancin masarautar a Istanbul. Har yanzu ba a samo gawarsa ba.

Biyan yi wa yayansa hudu, maza biyu da mata biyu “na daga cikin kokarin da Saudiyya ke yi na ganin ta cika dogon yarjejeniyar da ta shiga da ahlin gidansa, duk a cikin kokarin ganin sun daina ci gaba da kalubalantar gwamnati a jawabansu,” cewar rahoton.

Masarautar Saudiyya ta biya yaran dan jaridar da aka kashe makudan kudade – Rahoto
Masarautar Saudiyya ta biya yaran dan jaridar da aka kashe makudan kudade – Rahoto
Asali: Depositphotos

Gidajen da aka ba yaran Kashogghi na a birnin Jeddah kuma sun kai kimanin dala miliyan hudu, jaridar ta ruwaito.

Rahoton ya kara da cewa, Salah, babban dansa, na shirin ci gaba da zama a masarautar, yayinda sauran da ke zaune a kasar Amurka, za su siyar da gidajen.

KU KARANTA KUMA: Da yiwuwar za mu fara siyar da man fetur sama da N145 - IPMAN

Bugu da kari, yaran na karban $10,000 ko sama da haka a duk wata sannan kuma suna iya samun Karin kudi da zai kai miliyoyin dala kowanne.

An dai zargi yariman kasar saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman da hannu a kisan dan jaridan amma masarautar kasar tayi ikirarin cewa bai da hannu a ciki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel