Atiku ya fi Buhari sau dubu a wurina - in ji Obasanjo

Atiku ya fi Buhari sau dubu a wurina - in ji Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana tsohon mataimakin sa, Atiku Abubakar a matsayin mutumin da ya fi shugaba Buhari iya siyasa, wayewa da kuma koshin lafiya

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce, duk da cewa kowanne mutum tara ya ke bai cika goma ba, amma ya na da tabbacin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya fi shugaban kasa Muhammadu Buhari sau dubu.

A cewar tsohon shugaban kasar, Atiku wanda ya yi mishi mataimaki a lokacin da ya yi mulki, ya fi shugaba Buhari, ta fannin sannin kan siyasa, fannin tattalin arziki da kuma wayewa.

Atiku ya fi Buhari sau dubu a wurina - in ji Obasanjo
Atiku ya fi Buhari sau dubu a wurina - in ji Obasanjo
Asali: Facebook

Obasanjo ya bayyana hakan a karshen makon nan a lokacin da shugabannin jam'iyyar PDP na yankin kudu maso yamma su ka kai masa wata ziyara, a gidansa da ke garin Abeokuta, cikin jihar Ogun.

KU KARANTA: A karo na farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano

Idan ba ku manta ba a wata wasika da tsohon shugaban kasar ya rubuta, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da lafiyar da zai iya mulkar Najeriya.

Duk da irin zaman da ke tsakanin tsohon shugaban kasar da mataimakinsa, sai gashi a zaben da ya gabata tsohon shugaban kasar ya na nu na goyon bayansa a gareshi, domin su hada karfi da karfe wurin cire shugaba Buhari daga kujerar da ya ke kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel