An kashe wata 'yar Najeriya da aka kama tana safarar kwayoyi a Saudiyya

An kashe wata 'yar Najeriya da aka kama tana safarar kwayoyi a Saudiyya

- Matsalar safarar miyagun kwayoyi dai na kara karfafa a duniya

- Sai dai kasar Saudiyya ta yi alkawarin kashe duk wani wanda ta kama yana safarar kwayoyi a kasar

Wani kamfanin dillancin labarai a kasar Saudiyya ya bayyana cewa an kashe wata mata 'yar Najeriya da ta ke zaune a kasar Saudiyya bayan kama ta da hukumar kasar ta yi tana safarar miyagun kwayoyi.

An kashe matar ne, ita da wasu maza guda biyu 'yan asalin kasar Pakistan da kuma wani namiji guda daya dan kasar Yemen. An yanke musu hukuncin kisan ne a birnin Makka, birni mafi tsarki a duniya.

An kashe wata 'yar Najeriya da aka kama tana safarar kwayoyi a Saudiyya
An kashe wata 'yar Najeriya da aka kama tana safarar kwayoyi a Saudiyya
Asali: Facebook

Kamfanin dillancin labaran ya bayyana cewa, a iya wannan shekarar kawai an kashe mutane sama da 52.

Kasar Saudiyyan dai ta yi kunnen kashi duk kuwa da irin matsin lambar da ta ke samu daga wasu manyan kungiyoyin kare hakkin dan adam na duniya, na bukatar ta kawar da hukuncin kisa.

KU KARANTA: 'Tun ina 'yar shekara 8 mahaifina ke kwanciya da ni'

Kasar ta Saudiyya ta yankewa mutane masu dinbin yawa hukuncin kisa, ciki kuwa har da wasu daga cikin 'yan kungiyar kare hakkin dan Adam da kuma 'yan ta'adda da aka kama su da laifi.

Idan ba a manta ba a bara kasar ta yi kokarin yankewa wata mata mai fafutukar kare hakkin mata, mai suna Israa Al-Ghomgham wacce rahoto ya nuna cewa ita ce mace ta farko 'yar asalin kasar Saudiyya da ta fara fuskantar hukuncin kisa saboda ayyukan da ta ke na hare hakkin mata na duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel