Ziyarar kungiyar CAN fadar shugaban kasa ta bar baya da kura

Ziyarar kungiyar CAN fadar shugaban kasa ta bar baya da kura

- Wani dan karamin sabani ya barke a ranar Litinin kan ziyarar da kungiyar kiristocin Nigeria (CAN) ta kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa

- Baya ga haka, ta kara jaddada cewa NCEF ba ta da wani karfin iko na yin magana a madadin sauran al'ummar kirista

- A cewar NCEF, babu wani bangare na majami'ar katolika da suka shiga sahun tawagar masu kaiwa Buhari ziyara

Wani dan karamin sabani ya barke a ranar Litinin kan ziyarar da kungiyar kiristocin Nigeria (CAN) ta kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa. Shugaban kungiyar CAN Samson Ayokunle ne ya jagoranci tawagar, wacce kungiyar dattawan kiristoci ta kasa (NCEF) ta bayyana a matsayin "lamari mai matukar girgizarwa."

CAN, ta ce kungiyar NCEF bai kamata ta taya shugaban kasa Buhari murnar lashe zaben ranar 23 ga watan Fabreru ba.

Sai dai kungiyar CAN ta jaddada cewa za ta ci gaba da zama maras nuna bangaranci a siyasa, tana mai cewa tunda dai hukumar zabe ta bayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben, ba ta da wani ikon bijirewa hakan.

KARANTA WANNAN: Kotu ba za ta hana INEC ci gaba da karbar sakamakon zaben Rivers - Inyang Ekwo

Ziyarar kungiyar CAN fadar shugaban kasa ta bar baya da kura
Ziyarar kungiyar CAN fadar shugaban kasa ta bar baya da kura
Asali: Facebook

Baya ga haka, ta kara jaddada cewa NCEF ba ta da wani karfin iko na yin magana a madadin sauran al'ummar kirista, "an haramta mata wannan".

Kungiyar NCEF ta cire kanta daga cikin wannan ziyara, tana mai ikirarin cewa ba za ta tsoma baki ba kasancewar lamarin zaben shugaban kasar yana kotu. "Domin haka zai zama kamar kauyanci wani yaje yana taya Buhari murnar cin zabe, sakamakon zaben da yanzu haka yana kotu."

Kungiyar ta ce ziyarar, wacce aka yi a makon da ya gabata, ba a yi ta da yawun al'ummar kirista ba. A cewar NCEF, babu wani bangare na majami'ar katolika da suka shiga sahun tawagar masu kaiwa Buhari ziyara.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel