Tattara sakamakon Rivers: Rundunar yan sanda za ta tura jami’anta, za a rufe hanyar Aba

Tattara sakamakon Rivers: Rundunar yan sanda za ta tura jami’anta, za a rufe hanyar Aba

- Hukumar yan sanda ta sanar da cewar ce ta soma tura jami’anta zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe domin tsaron tattara sakamakon zabe da za a fara a jihar a ranar Alhamis

- Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar 21 ga watan Maris, ta bayyana cigaba da tattara sakamako da bayyana sakamakon a jihan tsakanin ranar 2 zuwa 5 ga watan Afrilu

- Za a rufe hanyoyin Waterlines da GRA dake babbar titin Port Harcourt/Aba a lokacin da za a gudanar da ayyukan tattara kuri’un

Rundunan yan sanda reshen jihar Rivers a ranar Litinin ta ce ta soma tura jami’anta zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe domin tsaron tattara sakamakon zabe da za a fara a jihar a ranar Alhamis.

Kakakin rundunan, DSP Nnamdi Omoni, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar a Port Harcourt a ranar Litinin.

Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar 21 ga watan Maris, ta bayyana cigaba da tattara sakamako da bayyana sakamakon a jihan tsakanin ranar 2 zuwa 5 ga watan Afrilu.

Tattara sakamakon Rivers: Rundunar yan sanda za ta tura jami’anta, za a rufe hanyar Aba
Tattara sakamakon Rivers: Rundunar yan sanda za ta tura jami’anta, za a rufe hanyar Aba
Asali: UGC

A cewar Omoni, an yanke shawaran tura jami’ai ne bayan ganawa a tsakanin kwamishinan yan sandan jihar da kuma kwamitin tattaunawa kan tsaron zabe (ICCES).

Omoni ya bayyana cewa za a rufe hanyar yankin mahadin Waterlines da GRA dake babbar titin Port Harcourt/Aba a lokacin da za a gudanar da ayyukan tattara kuri’un.

KU KARANTA KUMA: Daukar ma’aikata na 2019: Rundunar sojin ruwa ta bayyana ranar jarabawa

Ya bayyana cewa za a rufe dukkan hanyoyin, cewa masu amfani da hanyan su canja hanya zuwa hanyoyin Olu Obasanjo da Polo Club.

Kakakin rundunan yan sandan yayi gargadin cewa duk wani ko kungiya da aka kama suna kokarin ta da zaune tsaye zasushiga hannun hukuma kamar yanda dokar zabe ta tanadar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel