Kotu ba za ta hana INEC ci gaba da karbar sakamakon zaben Rivers - Inyang Ekwo

Kotu ba za ta hana INEC ci gaba da karbar sakamakon zaben Rivers - Inyang Ekwo

- Wata kotu ta yi fatali da wata bukata da aka gabatar a gabanta na dakatar da INEC daga ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Rivers

- Mai shari'a Inyang Ekwo a hukuncin da ya yanke, ya ce kotun ba ta da wani hurumi na ci gaba da sauraron karar

- Mai shari'ar ya ce kotun sauraron korafe korafen zabe ce kadai ke da hurumin karbar korafin zabe ba wai babbar kotun tarayya ko ta jiha ba

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Abuja, ta yi fatali da wata bukata da aka gabatar a gabanta na dakatar da hukumar zaben kasar INEC daga ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Rivers da aka kada a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

Mai shari'a Inyang Ekwo a hukuncin da ya yanke, ya ce kotun ba ta da wani hurumi na ci gaba da sauraron karar.

Mai shari'a Ekwo a ranar 20 ga watan Maris ya ki amincewa da karbar wata bukata da dan takarar gwamnan jihar Rivers karkashin jam'iyyar ACC, Mista Biokpomabo Awara na hana INEC ci gaba da karba tare da sanar da sakamakon zaben jihar da aka kammala ba tare da jin ta bakin INEC ba.

KARANTA WANNAN: Allah ya tsare: Yadda aka yi garkuwa da wasu masu kasuwancin gawayi a Kaduna

Kotu ba za ta hana INEC ci gaba da karbar sakamakon zaben Rivers - Inyang Ekwo
Kotu ba za ta hana INEC ci gaba da karbar sakamakon zaben Rivers - Inyang Ekwo
Asali: Depositphotos

A mai makon hakan, mai shari'ar ya bukaci INEC da ta zamo a cikin shiri. Bayan sauraron karar, mai shari'ar ya ce babu wata kwakkwarar hujja akan karar, don haka ya yi watsi da ita.

Da ya ke yanke hukunci, mai shari'a Inyang Ekwo, ya bayyana cewa ma damar an gudanar da zabe, to babbar kotun gwamnatin tarayya ko ta jiha ba za ta iya nuna karfin ikon shari'a akan amarin ba, kasancewar wannan aikin kotun sauraron korafe korafen zabe ne.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel