Da yiwuwar za mu fara siyar da man fetur sama da N145 - IPMAN

Da yiwuwar za mu fara siyar da man fetur sama da N145 - IPMAN

Kungiyar masu kasuwanci man fetur masu zaman kansu a Najeriya (IPMAN) ta bukaci gwamnatin tarayya da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) da ta tabbatar da cewa mamallakan manyan tankunan sauke mai sun ci gaba da samunsa akan farashin da na N133.28 kan kowace lita.

Shugaban IPMAN, Mista Shina Amoo, wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Lagas a ranar Litinin, ya bayyana cewa masu kasuwanci mai na iya fara siyawar sama da N145 kan kowace lita idan har masu manyan tankunan sauke mai suka ci gaba da siyarwa akan N136.5 da N137 kan kowace lita.

Amoo ya bukaci NNPC da ta tursasa masu manyan tankunan sauke mai da kada su siyar sama da farashin da ake siyarwa a da domin ba yan kasuwa dammar siyarwa abokan cinikinsu akan N145 kowace lita.

Da yiwuwar za mu fara siyar da man fetur sama da N145 - IPMAN
Da yiwuwar za mu fara siyar da man fetur sama da N145 - IPMAN
Asali: UGC

Ya kuma yaba ma gwamnatin tarayya akan inganta cibiyar man fetur na NNPC da ke Ilorin yayinda ya bukaci da ta gyara na Ore domin rage matsalar zirga-zirgan man fetur da kuma samar da Karin ayyuka a yankin.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa bamu tabbatar da Magu ba – Saraki

A wani jawabi da ya saki a ranar 30 ga watan Maris, manajan darakta na NNPC, mai kula da harkokin jama’a, Mista Ndu Ughamadu ya gargadi mamallakan tankunan sauke mai da kada su kara farashin mai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel