Kada ku tsaya a wajen majalisar dokokin kasar a ranar rantsarwa – Saraki ga zababbun yan majalisa

Kada ku tsaya a wajen majalisar dokokin kasar a ranar rantsarwa – Saraki ga zababbun yan majalisa

Shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya ja hankalin zababbun yan majalisar dokokin kasar da kada su tsaya a wajen majalisa a ranar rantsarwa kamar yanda wasu sanatoci suka yi a 2015.

Saraki, wanda yayi magana a lokacin taron wayar da kan zababbun yan majalisar dokoki a Abuja a ranar Litinin, yace ana taron rantsarwar ne a zauren majalisun kasar guda biyu ba wai a wani waje na daban ba.

Saraki yayi maganan ne sakamakon al’amarin da ya auku a 2015, a lokacin da shugaban APC na kasa a wancan lokacin ya kiran taron gaggawa a babban dakin taro na kasa (ICC), tare da sanatoci goma da mambobi goma a ranar 9 ga watan Yuli, 2015, a lokacin da ya kamata ayi bikin rantsarwar.

Kada ku tsaya a wajen majalisar dokokin kasar a ranar rantsarwa – Saraki ga zababbun yan majalisa
Kada ku tsaya a wajen majalisar dokokin kasar a ranar rantsarwa – Saraki ga zababbun yan majalisa
Asali: Depositphotos

Haka zalika, kadan daga ikin mambobin APC, har da Saraki da kakakin majalisa Yakubu Dogara, har da wassu mambobin PDP ne suka tsaya a zauren majalisar. Wannan lamarin ne yayi sanadiyan fitowar Saraki a matsayin shugaban majalisa ba tare da adawa ba, sannan Ike Ekweremadu, na PDP ya fito a matsayin mataimakin shugaban majalisa duk da kasancewar APC ce mafi rinjaye a majalisar.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa bamu tabbatar da Magu ba – Saraki

Yan majalisan sun yabi Saraki akan bayyana ra’ayinsa da yayi.

Yayinda Dogara ya sake lashe zabe a majalisan don cigaba da wakiltan al’umman mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa dake jihar Bauchi, Saraki ya sha kayi a yunkurinsa na dawowa majalisan yayinda Ibrahim Yahaya Oloriegbe na APC yayi nasara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel