Da duminsa: Shugaba Bouteflika na Algeria zai yi murabus kafin ranar 28 ga Afrelu

Da duminsa: Shugaba Bouteflika na Algeria zai yi murabus kafin ranar 28 ga Afrelu

- Shugaban kasar Algeria Abduleziz Bouteflika zai yi murabus kafin karewar wa'adin mulkinsa a ranar 28 ga watan Afrelu

- Miliyoyin 'yan Algeria ne suka gudanar da zanga zanga inda suke kira ga Bouteflika mai shekaru 82 da ya yi murabus bayan shafe shekaru 20 yana mulki

- Duk da wannan matsaya ta Bouteflika na yin murabus, har yanzu dai daliban kasar Algeria na ci gaba da kira da a kara yawaita yin zanga zanga

Shugaban kasar Algeria Abduleziz Bouteflika zai yi murabus kafin karewar wa'adin mulkinsa a ranar 28 ga watan Afrelu, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa, wacce kuma kamfanin dillancin labarai na APS ya dauka.

Shugaban kasar zai dauki wannan matakin ne "domin tabbatar da cewa dukkanin ma'aikatu sun ci gaba da aiki a yayin mika mulki," a cewar sanarwar wacce aka raba a ranar Litinin, tana mai cewa, murabus dinsa "zai gudana ne kafin ranar 28 ga watan Afrelu, 2019."

Miliyoyin 'yan Algeria ne suka gudanar da zanga zanga na mako guda a fadin kasar inda suke kira ga shugaban kasar mai shekaru 82 da ya yi murabus bayan shafe akalla shekaru 20 a kan karagar mulki. Tun bayan shanyewar rabin jikinsa a 2013 aka daina ganinsa a bainar jama'a sosai.

KARANTA WANNAN: Dalilin dakatar da zana jarabawar shiga makarantar horas da sojoji ta Kaduna - NDA

Da duminsa: Shugaba Bouteflika na Algeria zai yi murabus kafin ranar 28 ga Afrelu
Da duminsa: Shugaba Bouteflika na Algeria zai yi murabus kafin ranar 28 ga Afrelu
Asali: Twitter

A baya bayan nan ne dai ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na biyar, amma a ranar 11 ga watan Maris ya janye wannan kudiri na sa da kuma dage zaben kasar, da aka shirya gudanarwa a ranar 18 ga watan Afrelu, la'akari da yawaitar zanga zanga a kasar.

Duk da wannan matsaya ta Bouteflika na yin murabus, har yanzu dai daliban kasar Algeria na ci gaba da kira da a kara yawaita yin zanga zanga musamman babbar zanga zanga a ranar Talata a babban birnin kasar da ma sauran sassa na kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel