Dalilin da yasa bamu tabbatar da Magu ba – Saraki

Dalilin da yasa bamu tabbatar da Magu ba – Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a jiya Litinin, 1 ga watan Afrilu yayi bayanin dalilin da yasa majalisar dattawa ta ki tabbatar da Mista Ibrahim Magu a matsayin Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Saraki ya bayyana cewa da tuni sun tabbatar da nadin Magu amma sun gaza yin hakan ne saboda fadar Shugaban kasa ta ki binciken zauren da ya kamata.

Baya ga haka, ya bayyana cewa kamata yayi ayi amfani da “mafitar siyasa” bayan majalisar dattawa ta ki amincewa da shi sau biyu.

Shugaban majalisar dattawan yayi Magana ne a wani shirin wayar da kai da aka shirya domin zababbun sanatoci da zababbun yan majalisar wakilai gabanin rantsar da yan majalisar dokokin kasar na tara a Abuja.

Dalilin da yasa bamu tabbatar da Magu ba – Saraki
Dalilin da yasa bamu tabbatar da Magu ba – Saraki
Asali: Depositphotos

Saraki yayi yunkurin basar da tambayoyi akan dalilin da yasa majalisar dokkin kasar bata je kotu ba domin tabbatar da jawabi kan kin amincewa da nadin Magu a matsayin Shugaban EFCC.

Don haka an tursasa shi yin martani lokacin da aka ta nanata tambayar.

Saraki ya bayyana cewa dabara ta rage ga bangaren zartarwa ta nemo wanda zai maye gurbin wani da aka ki tabbatarwa.

KU KARANTA KUMA: Ina fargabar abin da zai kasance da jam'iyyar APC a 2023 - Okorocha

Da yake magana mussamman akan zabar Magu, ya bayyana cewa babu makawa cewa majalisar dattawa na da ikon tabbatar dashi ko kuma ta yi watsi da zabar shi.

Kan dalilin da yasa majalisar bata je kotu ba, yace akwai shari’a sama da 12 a kotu kan lamarin.

Saraki, wanda yace wasu daga cikin shari’an na kotu sama da shekaru biyu, ya kara da cewa ba zai iya bayani kan dalilin da yasa ba a yanke hukunci kan lamarin ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel