Hattara dai: Wasu mutane na kokarin kunna wutar rikici a Kaduna

Hattara dai: Wasu mutane na kokarin kunna wutar rikici a Kaduna

Shugaban karamar hukumar Sanga ta jahar Kaduna, Mista Charles Danladi ya bayyana cewa sun bankado shirin wasu mutane na kitsa rikicin addini tare da tayar da hankali a jahar Kaduna, don haka yake kira ga hukumomin tsaro sun tashi tsaye.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Danladi ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu inda yace sun samu ingantattun bayanai dake nuna mutanen sun shirya tayar da rikicin daga karamar hukumar Sanga.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Hattara dai: Wasu mutane na kokarin kunna wutar rikici a Kaduna
Hajiya Hadiza da El-Rufai
Asali: UGC

Danladi yace miyagun mutanen sun shirya tayar da rikicin a Sanga ne kasantuwar daga nan mataimakiyar gwamnan jahar Kaduna, Hajiya Hadiza Balarabe ta fito, don haka suke so suyi amfani da dalilin cewa Hajiya Hadiza na kokarin tsige shugaban karamar hukumar saboda shi Kirista ne.

“Ina sanar daku shirin da wasu mutane suke yi na kitsa rikicin addini a karamar hukumar Sanga, tare da kira a gareku daku tashi tsaye don tabbatar da tsaro a karamar hukumar nan, mutanen sun yi taro a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris a garin Kaduna, kuma sun turo kudi zuwa Sanga don gudanar da zanga zanga a ranar ranar Talata, 2 ga watan Afrilu.

“Rahotannin da muka samu sun nuna mutanen nan na kokarin raba kawunan jama’a ta hanyar amfani da addini a karamar hukumar Sanga sakamakon Hajiya Hadiza mataimakiyar gwamnan jahar Kaduna yar Sanga ce.

“Don haka sun shirya watsa jita jitan wai Hajiya Hadiza na kokarin ganin ta tsige shugaban karamar hukumar Sanga saboda shi Kirista ne ba Musulmi ba, ta haka sai su tayar da rikici. Ina fada muku cewa bani da wata matsala da Hajiya Hadiza a matsayina na shugaban karamar hukumar Sanga.” Inji shi.

Daga karshe Danladi ya bayyana cewa karamar hukumar Sanga za tayi iya bakin kokarinta tare da taimakon gwamnatin jaha da hukumomin tsaro don su tabbatar da zama lafiya a yankin, da ma jahar gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel