Hawaye ya kwaranya yayinda yan Shi'a sukayi taron tunawa da mamatansu 998

Hawaye ya kwaranya yayinda yan Shi'a sukayi taron tunawa da mamatansu 998

Hawaye sun kwaranya ranar Litinin a birnin tarayya Abuja yayinda daruruwan yan kungiyar mabiya akidar Shi'a suka taru domin tunawa da mamatansu da "jami'an tsaro suka kashe a fadin tarayya."

Wannan taro da aka gudanar a farfajiyar 7 Uption Garden Garki, Abuja, ya cika da takaici, hawaye da bakin cikin yayinda suka rike da hotunan yan uwansu da aka hallaka.

Shugaban gidauniyar Shuhada, Sheikh AbdulHameed Bello, wanda ya gabatar da jawabi ga mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, a taron ranan shahidai ya ce kungiyar ta yi rashin mambobi 998 sakamakon "kisan gillan da Soji da yan sanda ke musu".

Hawaye ya kwaranya yayinda yan Shi'a sukayi taron tunawa da mamatansu 998
Yan shia
Asali: Facebook

Bello ya ce an kafa gidauniyar Shuhada ne domin kula da marayu, mata, iyaye, da ya uwan wadanda suka rasa rayukansu. Ya kara da cewa gidauniyar na daukan nauyin karatun yaransu daga matakin rauda har jami'a.

"Muna biyan kudin jinyan duk wanda ke rashin lafiyar cikinsu. Muna kula da jin dadinsu irin daurin aure da bikin Sallah." Ya ce.

Hawaye ya kwaranya yayinda yan Shi'a sukayi taron tunawa da mamatansu 998
Hawaye ya kwaranya yayinda yan Shi'a sukayi taron tunawa da mamatansu 998
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Yar Shi'a, wacce aka kashewa 'yaya 5, na shida na kwance da harasasai cikin kirjinsa, ta ce babu gudu, ba ja da baya

Hawaye ya kwaranya yayinda yan Shi'a sukayi taron tunawa da mamatansu 998
Hawaye ya kwaranya yayinda yan Shi'a sukayi taron tunawa da mamatansu 998
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel