Yan Boko Haram sun bankawa kauyen Chibok wuta

Yan Boko Haram sun bankawa kauyen Chibok wuta

Wasu yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun sake kai hari karamar hukumar Chibok dake jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya. Wannan hari ya biyo bayan hare-hare da kona gidajen da yan ta'ddan suka kai kwanaki uku baya garin Gatamwarma da Chibok.

Wata majiya mai karfi ta bayyawana The Cable cewa an kai harin ne yayinda rundunar sojin 117 Batallion suke shirin shiga kauyen Kaumutiyahi.

Majiyar tace: "A gaskiya akwai Soji a hanyar kimanin kilomita shida da garin da aka hari, amma za su bukaci karin runduna."

Wani mazaunin Chibok ya bayyana cewa: "Sun shigo ta dajin Sambisa misalin karfe 7 na dare kuma tun lokacin suke bankawa kauyen wuta."

KU KARANTA: 'Yar Shi'a, wacce ake kashewa 'yaya 5, na shida na kwance da harasasai cikin kirjinsa, ta ce babu gudu, ba ja da baya

A watan Disamba, yan ta'addan sun kai hari kauyen Makalama dake Gatamawarwa. Sannan suka kai hari Bwalakia kwanaki uku bayan haka, inda suka kona gidajen mutane.

Daya daga cikin wanda abin ya shafa yace: "Sun sace mana dukkan abinda muke da shi kuma suka kona gidan. Bamu da abinci, bamu da wajen kwana."

Za ku tuna cewa a watan Nuwamban 2018, Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi ya bayyana cewa jama'ar yankin Chibok na karkashin Boko Haram har yanzu.

A lokacin da muke kawo wannan rahoto, kakakin hukumar Soji, Sagir Musa, bai yi tsokaci kan harin ba yayinda aka tuntubeshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel