Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Gungun miyagu yan bindiga sun kai farmaki akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, inda suka tare motoci da dama tare da yin awon gaba da matafiya da dama zuwa cikin dazuka da nufin yin garkuwa dasu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi sanadiyyar aukuwar hadarurruka da dama akan babbar hanyar yayin da suka tilasta ma motoci tsayawa duk kuwa da mugun gudun da wasu motocin ke yi, sa’annan sun kwace kudade, wayoyi da sauransu.

KU KARANTA: Yan Firamari na cin shanu 594, kaji 148,000 da kwai miliyan 6.8 – Inji Osinbajo

Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Motoci a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Asali: UGC

Wani shaidan gani dai do, Yakubu Muhammed ya bayyana ma majiyarmu cewa jim kadan da aukuwar lamarin sai ga Sojoji cike da manyan motoci guda uku, tare da jami’an Yansanda, amma ko kafin su zo yan bindigan sun yi tafiyarsu.

Muhammed yace yana kan hanyarsata zuwa Legas daga Kaduna a cikin wata babbar kotar Luxirious Bus ne a lokacin da suka tarar da yan bindigan sun tare hanyar a daidai kauyen Katari da misalin karfe 6:22 na yamma.

A cewarsa, yan bindigan sun kwashe sama da mintuna 30 suna cin karensu babu babbaka, domin kuwa koda Sojoji da Yansanda suka isa wajen, tuni yan bindigan sun yi awon gaba da mutane da dama zuwa cikin dazuka.

Wasu daga cikin motocin da yan bindigan suka kwashe fasinjojinsu gaba daya akwai Totoya Hilux, da Toyota Corolla Sedan, yayin da aka hangi wasu motoci da dama da suka sha harbe harben bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel