Gwamna Ganduje ya bayyana abinda zai faru da PDP idan har ta kai kararsa gaban Kotu

Gwamna Ganduje ya bayyana abinda zai faru da PDP idan har ta kai kararsa gaban Kotu

Zababben gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna ma jam’iyyar PDP yatsa, tare da gargadinta game da abinda zai biyo baya idan har ta garzaya gaban kotu akan kalubalantar nasarar daya samu a zaben daya gudana makonni biyu da suka gabata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ganduje yace jam’iyyar PDP za tayi da-na-sanin kalubalantar nasararsa data shirya yi a gaban kotu, haka nan kuma wannan matakin da suke shirin dauka zai tarwatsa jam’iyyar kanta.

KU KARANTA: Yan Firamari na cin shanu 594, kaji 148,000 da kwai miliyan 6.8 – Inji Osinbajo

Gwamna Ganduje ya bayyana abinda zai faru da PDP idan har ta kai kararsa gaban Kotu
Gwamna Ganduje
Asali: Depositphotos

Ganduje ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin dubun dubatan masoya da magoya baya da suka fito kai masa ziyara daga garin Ganduje, cikin karamar hukumar Dawakin Tofa a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labaru na jahar Kano, Muhammad Garba ya fitar, inda yace cewa “Kafin zaben makon daya gabata da muka yi nasara, PDP ta yi amfani da magudin iri iri wanda daga bisani muka bankadosu.

“Amma daga bisani da aka yi zaben gaskiya da gaskiya, kuma aka hanasu daman yin magudi, ai kaga sahihan sakamakon da zabukan suka nuna, don haka nake ganin sun gab da daukan matakin da zai lalatasu gaba daya, kaikayi zata koma kan mashekiya.

“Zamu duba irin magudin da suka tafka a sauran zabukan yan majalisu, tare da duba ingancin kuri’un da suke ikirarin sun samu ko akasin haka.” Inji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A wani labarin kuma, gwamnan yace bashi da nufin yin barazana ko cin fuska ga wani mutum ko yan adawa a jahar Kano, a iya zangon mulkinsa na shekaru hudu masu zuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel