'Yar Shi'a, wacce aka kashewa 'yaya 5, na shida na kwance da harasasai cikin kirjinsa, ta ce babu gudu, ba ja da baya

'Yar Shi'a, wacce aka kashewa 'yaya 5, na shida na kwance da harasasai cikin kirjinsa, ta ce babu gudu, ba ja da baya

Hajiya Jummai Karofi, wata yar kungiyar mabiya akidar Shi'a ta bayyana yadda aka hallaka 'yayanta biyar a rikicin Sojoji da yan shi'a da ya faru a watan Disamban 2015 inda aka kashe daruruwan mabiya kungiyar.

Ta laburta abinda idonta ya gani ranar Litinin a birnin Abuja inda aka gudanar da taron tunawa da mambobin da suka rasa rayukansu a gwagwarmaya.

Hajiya Jummai ta ce an harbe mata 'yaya biyar a Zaria, sannan na shidan na kwance a asibiti sakamakon harbin bindiga da harsasai a kirjinsa.

Ta bayyana cewa duk da abinda ya faru da ita, babu ba ja da baya. Ko kiris hakn bai rage mata imani ba.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya isa kasar Senegal (Hotuna)

Tace: "Babu wani kasa a gwiwa a wannan gwagwarmayan. Ko a tarihi, duk wadanda suka yaki zalunci, ko ba na addini ba, suna fuskantar kalubale daga azzaluman. Saboda haka mafita shine jajircewa, sadaukar da komai domin samun abinda kake so."

"Kuma a kan wannan zamu rayu kuma mu mutu. Ba zamu taba ja da baya ba. Wannan alkawari ne."

"Yau muna tunawa da matattunmu. A matsayina ta uwa, na yi rashin yara biyar a rikicin Zaria kuma daya daga cikin yayanda dauke da harsashi cikin kirjinsa a yanzu. Ni kaina, an sha harbi na; kamar yadda ka gani, sai da aka rikeni saboda azaba da nike sha."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel