Yan Firamari na cin shanu 594, kaji 148,000 da kwai miliyan 6.8 – Inji Osinbajo

Yan Firamari na cin shanu 594, kaji 148,000 da kwai miliyan 6.8 – Inji Osinbajo

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na ciyar da daliban fimarin Najeriya abinci daban daban a karkashin tsarin jam’iyyar APC na ciyarwa, kamar yadda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana.

Legit.ng ta ruwaito Osinbajo yace gwamnatin na ciyar da daliban shanu dari biyar da casa’in da hudu, kaji dubu dari da arba’in da takwas, kwai miliyan shida da dubu dari takwas da kuma tan tamanin da uku da kifi, a kowanni mako.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya 5 da suka yi karatu a jami’ar Maiduguri

Yan Firamari na cin shanu 594, kaji 148,000 da kwai miliyan 6.8 – Inji Osinbajo
Osinbajo
Asali: Facebook

Osinbajo ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a bikin yaye daliban jami’ar Legas karo na hamsin daya gudana a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, inda yace gwamnati na kashe dala 0.19 akan ciyar da kowanne dalibi a kowanne rana.

Hakanan ya kara da cewa dalibai miliyan tara da dubu dari uku da dari takwas da casa’in da biyu, 9,300,892 ne suke cin gajiyar tsarin ciyarwar a makarantu dubu arba’in da dari takwas da talatin da bakwai,49,837, a jahohi ashirin da shida.

Mataimakin shugaban ya cigaba da cewa sun dauki ma’aikata masu dafa abinci dubu casa’in da biyar da dari hudu da ashirin da biyu a karkashin tsarin, 95,422, sa’annan akwai kananan manoma sama da dubu dari da gwamnati ke sayan kayan Kadin hadin abincin daga wajensu.

Daga karshe Osinbajo ya bada tabbacin abincin da ake ciyarwar na kunshe da duk sinadaran da dalibi yake bukata, kuma ana sa ran kara yawan jahohin dake cin gajiyar tsarin ciyarwar zuwa karshen shekara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel