Jiragen yakin Najeriya sun tafka ma yan bindiga mummunar barna a jahar Zamfara

Jiragen yakin Najeriya sun tafka ma yan bindiga mummunar barna a jahar Zamfara

Dakarun rundunar mayakan sojan saman Najeriya sun dakile wani yunkurin kaddamar da hari da wasu gungun yan bindiga suka yi a wasu kauyukan jahar Zamfara, a kokarinsu na kawo karshen ayyukan yan bindigan a jahar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tarwatsa aniyar yan bindigan ne ta hanyar amfani da jiragen yaki wajen yi ma yan bindigan aman wuta daga sama a daidai lokacin da suka yi kokarin kutsa kai cikin kauyukan Hayin Mahe da Hayin Kanawa a karamar hukumar Gusau.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya 5 da suka yi karatu a jami’ar Maiduguri

Kaakakin rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, inda yace Sojojin sun kai ma yan bindigan hari ne a ranar Lahadin data gabata bayan samun bayanan sirri dake nuna yan bindiga daga dajin Sububu da Kagara sun afka kauyukan biyu.

Ko kafin Sojoji su isa kauyukan, yan bindigan har sun fara hare hare a kauyukan, tare da tattara wasu mutane da zasu yi awon gaba dasu, isarsu keda wuya, sai aka fara batakashi tsakaninsu da yan bindigan, inda nan da nan suka tsere zuwa cikin daji.

“Amma Sojojin basu yi kasa a gwiwa ba, inda suka bi sawunsu zuwa cikin daji tare da yi musu rakiyar kura har sansaninsu dake dajin Sububu, a can suka kashe yan bindiga guda biyar, tare da jikkata wasu kuma da dama, Sojoji sun kwato bindigu 3 kirar AK47, da alburusai da dama.” Inji shi.

Haka zalika kaakakin yace sun ceto wasu mata biyu da karamin yaro daya da yan bindigan suka yi awon gaba dasu, inda tuni suka mikasu ga mai garin Mada bayan sun koma kauyukan domin basu kariya daga yiwuwar sake afka musu.

Daga karshe kaakaki Daramola ya bada tabbacin rundunar sojan sama na cigaba da aikin kakkabe ragowar yan bindigan da suka rage a yankin Zamfara, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel