Bai kamata APC ta nuna fifiko a kan kowa karara a zaben Majalisa ba – Kumalia

Bai kamata APC ta nuna fifiko a kan kowa karara a zaben Majalisa ba – Kumalia

Honarabul Mohammed Umara Kumalia, tsohon ‘Dan majalisar wakilai ne a Najeriya a karkashin jam’iyyar adawa. Kumalia yayi hira da Daily Trust a karshen makon jiya inda yayi magana game da takarar kujerun majalisa a zaben bana.

Umara Kumalia wanda yayi fice a majalisa ta 5, ya gargadi jam’iyyar APC mai mulki a game da matakin da ta dauka na kasa mukaman majalisa zuwa ga wasu tsirarrun ‘ya ‘yan jam’iyya. Hon. Kumalia yace sam ba haka ya dace APC tayi ba.

Honarabul Umara Kumalia yake cewa tsakanin 1999 zuwa 2007 lokacin da yake majalisa, abin da jam’iyya ta ke yi shi ne ta fitar da yankin da za su fito da wanda zai rike kowane mukami, bayan nan ne kuma sai a fito a gwabza, ayi takara.

Tsohon ‘dan majalisar yace a irin wannan tsari ne ya zama shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai daga jam’iyyar adawa ta ANPP a lokacin bayan da aka shirya cewa yankin sa na Arewa maso Gabas ce za ta kawo wannan kujera a lokacin.

KU KARANTA: Jigon APC ya roki Sanata Ndume ya janye takarar sa

Bai kamata APC ta nuna fifiko a kan kowa karara a zaben Majalisa ba – Kumalia
APC tace dole kowane Sanata ya marawa Lawan baya a zaben Majalisa
Asali: Depositphotos

Ta haka ne irin su Fidel Ayogu, Sule Yari Gandi da sauran ‘yan majalisun lokacin su ka tashi da manyan kujeru bayan an yi zabe. Kumalia yace irin wannan tsari ne kuma aka yi amfani da shi har a majalisar dattawa a tsakanin 1999 zuwa 2007.

Hon. Umara Kumalia yake cewa a ko yaushe ‘yan majalisa za su janye goyon baya ne ga wani na su da ake kokarin nuna fifiko a kan sa, domin su nuna irin isar da su ke da shi a majalisa, irin haka ne aka yi wajen zaben Aminu Tambuwal a 2011.

Fitaccen ‘dan siyasar ya nemi APC ta kasa kujerun majalisar zuwa shiyyoyi, sannan kuma ta kyale Sanatoci da ‘yan majalisa su zabi duk wanda su ke so daga wadannan yankuna ba wai a fito a tursasa masu cewa dole su zabi wane ko wane ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel