Sojoji sun kama wani kwararren injiniya da ke kera wa 'yan ta'adda amakamai

Sojoji sun kama wani kwararren injiniya da ke kera wa 'yan ta'adda amakamai

Hedikwatar rundunar soji ta OPWS (Operation Whirl Stroke) da ke aikin atisaye na musamman a jihohin Benuwe, Nasarawa da Taraba, ta sanar da kama wasu mutane biyu da take zargi da kera makamai a karamar hukumar Logo da ke jihar Benuwe.

Da yake jawabi ga manema labarai, kwamandan rundunar OPSW, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya bayyana cewar wata rundunar OPSW ce ta kama wadanda ake zargin a karamar hukumar Logo bayan samun wasu muhimman bayanan sirri.

Yekini ya bayyana cewardakarun soji sun shafe tsawon sati hudu kafin su gano mutanen da wurin da ake kera makaman bayan samun bayanai a kan haramtacciyar masana'antar.

Ya kara da cewa hedikwatar OPWS ce ta sanar da karamar rundunar su da ke karamar hukumar Logo bayan kammala dukkan muhimman bayanan da zasu kai ga kama masu muguwar sana'ar.

Sojoji sun kama wani kwararren injiniya da ke kera wa 'yan ta'adda amakamai
Sojoji
Asali: Twitter

A nasa bangaren, kwamandan karamar rundunar OPWS a yankin Logo, Kaftin Samuel Okinahi, ya ce sun sha wahala kafin su kamo masu laifin.

Ya ce sun samu makamai da dama a masana'antar da masu laifin ke kera su, ya ce masu laifin sun amsa cewar su na da abokan kasuwanci a jihohin Benuwe da Taraba.

Ya kara da cewa sun kama wadanda ake zargin a ranar 24 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara

Daya daga cikin masu kera makaman ya shaida wa manema labarai cewar shi kwararren injiniya ne da ya yi karatu a kasar Mauritania na tsawon shekara biyar kafin daga bisani ya dawo Najeriya.

Sannan ya kara da cewa a can kasar Mauritania ne ya koyi yadda ake kera makaman tare da bayyana cewar ya shiga muguwar sana'ar ne bayan duk kokarinsa na samun aiki da kafa kasuwanci bayan ya dawo Najeriya bai kai ga nasara ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel