Bukola Saraki yayi jawabi a gaban sababbin ‘Yan Majalisar Tarayya

Bukola Saraki yayi jawabi a gaban sababbin ‘Yan Majalisar Tarayya

Shugaban majalisar Najeriya, Dr. Bukola Saraki, yayi jawabi a gaban ‘yan majalisar tarayya a Ranar Lahadi, 31 ga Watan Afrilun 2019. Bukola Saraki yayi bayani ne domin shiryawa masu shirin shigowa majalisar wakilai da dattawa.

Majalisar ta shirya taro ne na musamman domin fara yi wa sababbin ‘ya ‘yan majalisa tanadin sanin kan aiki. Sai dai Bukola Saraki wanda shi ne shugaban majalisar dattawa ya rasa takarar da ya nema na sake komawa majalisa a bana.

1. ‘Yancin kan Majalisa

Bukola Saraki yayi jawabi a game da gashin-kan da ‘Yan majalisa su ke da ita a dokar Najeriya. Saraki yace babu wanda ya isa ya shiga gonar majalisa na yin dokoki da kuma wakiltar jama’a.

2. Rashin karfin Majalisa

Shugaban majalisar ya kuma yi magana game da rashin karfin da Majalisa ta ke da shi a cikin sauran bangarorin gwamnati. Saraki yace mulkin soja da aka rika yi ne ya kawo wannan matsalar.

KU KARANTA: Mu na jiran a kawo sunan wanda zai gaji Magu a EFCC - Saraki

Bukola Saraki yayi jawabi a gaban sababbin ‘Yan Majalisar Tarayya
Ibrahim Yahaya Oloriegbe ya doke Saraki a zaben 2019
Asali: Twitter

3. Aikin ‘Yan Majalisa

Haka kuma Bukola Saraki ya bayyanawa sababbin ‘yan majalisar cewa babban aikin da ke gaban su shi ne yaki da talauci da rashin gaskiya da kuma neman inganta tsaro da karfafawa talakawa.

4. Yin abin da ya dace

Saraki ya kuma bayyanawa sababbin ‘yan majalisar kasar cewa akwai bukatar su dage wajen yin abin da zai taimaki al’umma na rage yawan kudin haraji da kawo karshen satar amsar jarrabawa da sauran su.

5. Kokarin Majalisa ta 8

Sanata Saraki mai shirin barin gado ya bayyana irin kokarin da majalisar da ya jagoranta tayi na kawo sababbin dokoki. Saraki yace sun amince da kudirori 274 tare da sauranan korafi fiye da 192 a shekaru 3.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel