Har ila yau: Mayakan Boko Haram sun kara kai hari Chibok, sun kone gidaje

Har ila yau: Mayakan Boko Haram sun kara kai hari Chibok, sun kone gidaje

Mayakan Boko haram sun kara kai hari Kaumutiyah, wani gari dake karkashin karamar hukumar Chibok a jihar Borno.

Harin na zuwa ne kwana uku kacal da mayakan kungiyar suka kai wani harin tare da kone gidajen jama'a a garin Gatamwarwa da ke karamar hukumar ta Chibok.

"Sun fito ne daga dajin Sambisa da misalin karfe 7:00 na yamma, sun shigo gari, sun hau kone gidajen mutane," kamar yadda wani mazaunin Chibok ya shaida wa majiyar mu.

Kauyen Kaumutiyah, da mayakan suka kai harin, na da nisan kilomita 13 daga garin Chibok.

Har ila yau: Mayakan Boko Haram sun kara kai hari Chibok, sun kone gidaje
Mayakan Boko Haram sun kara kai hari Chibok, sun kone gidaje
Asali: Depositphotos

Jaridar TheCable ta rawaito cewar wata majiyar rundunar soji ta 117 dake garin Chibok ta sanar da ita cewar ta na shirin mayar da martani ga mayakan da har yanzu basu bar garin na Kaumutiyahi ba.

DUBA WANNAN: Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara

"Tabbas akwai sojoji a wani sansani da bai fi nisan kilomita 6 ba daga kauyen, amma gaskiya basu da yawa, suna bukatar gudunmawa kafin su tunkari mayakan," a cewar majiyar.

Jaridar TheCable ta ce Sagir Musa, kakakin rundun rundunar soji bai waiwayi sakon neman karin bayani da suka aika masa ba a kan harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel