Shugaban kasar Algeria Abdelazez Bouteflika ya yi murabus biyo bayan tsanantar zanga-zanga

Shugaban kasar Algeria Abdelazez Bouteflika ya yi murabus biyo bayan tsanantar zanga-zanga

Shugaban kasar Algeria, Abdelazez Bouteflika, ya yi murabus biyo bayan tsanantar zanga-zanga da 'yan kasar ke yi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar (APS) ya rawaito a yau, Litinin.

Zai bar kujerar sa ta mulki kafin karewar wa'adinsa a ranar 28 ga watan Afrilu.

Shugaban ya yanke shawarar yin murabus ne bayan daruruwan jama'a sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sabuwar gwamnatin sa a birnin Algiers, hedikwatar mulkin kasar Algeria.

Masu zanga-zangar na dauke da takardun da ke bayyana zabin sabbin nade-naden gwamnatinsa a matsayin wanda ya saba da bukatar jama'a.

Bouteflika ya ki canja matakin nada kan sa a matsayin ministan tsaron kasar Algeria a sabuwar gwamnatin rikon kwarya da ya kafa a ranar Lahadi duk da adawa da hakan da jama'a su ka nuna.

Gwamnatin rikon kwaryar karkashin jagorancin Noureddine Bedoui ta kunshi ministoci 27, da suka hada da wasu 6 daga tsohuwar gwamnati.

Shugaban kasar Algeria Abdelazez Bouteflika ya yi murabus biyo bayan tsanantar zanga-zanga
Shugaban kasar Algeria; Abdelazez Bouteflika
Asali: Twitter

Jam'iyyar adawa, 'Labour Party, a kasar Algeria ta bayyana kunshin gwamnatin rikion kwarya da Boteflika ya kafa a mtsayin tsohuwar gwamnati da tsohuwar fuska.

"Bamu san me ya yi la'akari da shi wajen zabar mutanen da ya nada ba, ya kafa sabuwar gwamnatin ne domin dorewar tsohuwar gwamnatinsa da ma fi rinjayen jama'a basa kauna," a cewar jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Ana wata ga wata: Wata matar aure mai suna Hajara ta mutu a dakin saurayin ta

Hatta tsohon firaministan kasar, Ali Benflis, wanda dan jam'iyyar adawa ne sai da ya soki kunshin sabuwar gwamnatin tare da bayyana shi da cewar, "wani haramtaccen yunkuri ne da ya fusata mutane."

A watan Maris ne Bouteflika ya nada Bedoui, tsohon ministan harkokin cikin gida, a matsayin firamista bayan shugaban kasar ya fasa yin takara a karo na biyar bayan jama'a sun gudanar da zanga-zangar nuna rahin amincewa da yin takarar sa saboda rashin koshin lafiya.

A 'yan kwanakin baya bayan nan, dubban 'yan kasar Algeria sun fito kn tituna domin gudanar da zanga-zangar neman Bourflika ya yi murabus tare da kuma neman yiwa tsarin siyasar kasar garambawul.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel