Ku kawar da bala-gurbi da munafukan cikinku kafin 2023 – Obasanjo ga PDP

Ku kawar da bala-gurbi da munafukan cikinku kafin 2023 – Obasanjo ga PDP

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bukaci jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da ta kawar da bala-gurbi da munafukan cikinta wanda a cewarsa, basu da jajirjewar da zai mayar da jam’iyyar ga martabarta da ta rasa.

Obasanjo ya bayyana cewa har yanzu shugabannin PDP sun damu da cikinsu da aljihunsu ne, inda ya yi al’ajabin dalilin da yasa wasu suka bar jam’iyyar yayinda sauran suka yanke imani bayan sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa.

Jigon kasar yayi Magana ne a yammacin ranar Lahadi, 31 ga watan Afrilu, lokacin da shugabannin PDP na kudu maso yamma karkashin jagorancin mataimakin Shugaban jam’iyyar (kudu maso yamma), Dr Eddy Olafeso suka ziyarce shi a gidansa da ke Abokuta, jihar Ogun.

Ku kawar da bala-gurbi da munafukan cikinku kafin 2023 – Obasanjo ga PDP
Ku kawar da bala-gurbi da munafukan cikinku kafin 2023 – Obasanjo ga PDP
Asali: UGC

Wadanda suka halarci taron sun hada da; Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Biodun Olujimi, zababbun sanatoci, Kola Balogun, Ayo Akinyelure, zababben dan majalisar wakilai (Ibarapa ta arewa da tsakiya), Hon Ajibola Muraina, tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oinlola, da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ta gargadi Malami akan zaben Rivers

Obasanjo ya fada ma bakinsa cewa halin da yan Najeriya ke ciki a yanzu na bukatar wata kakkausar murya a PDP domin karfafa damokardiyya.

Ya kuma caccaki gazawar shugabanci a kasar, inda yace Najeriya ba za ta taba ci gaba ba “idan ta ci gaba a yadda take.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel