Yanzu Yanzu: An kama jami’an yan sanda 3 akan mumunan harbi a Lagas

Yanzu Yanzu: An kama jami’an yan sanda 3 akan mumunan harbi a Lagas

- Rahotanni sun nuna cewa an tsare wasu jami’an yan sanda uku da ke da nasaba da harbe wani dan Najeriya a Lagas a ranar Lahadi

- Mutumin da abun ya shafa, Kolade Johnson, na kallon wasan kwallon kafa ne a unguwarsa da ke Mangoro a yammacin ranar Lahadi lokacin da wata motar sintiri na yan sanda ta iso yankin don yin kame

- Yanayin shigar mutumin ne yasa su zargin shi mai laifi ne

An tsare wasu jami’an yan sanda uku da ke da nasaba da harbe wani dan Najeriya a Lagas a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mutumin da abun ya shafa, Kolade Johnson, na kallon wasan kwallon kafa ne a unguwarsa da ke Mangoro a yammacin ranar Lahadi lokacin da wata motar sintiri na yan sanda ta iso yankin don kama wani mutum.

A bisa ga idon shaida, yan sandan sun zargi mutumin da kasancewa mai laifi saboda yanayin shigarsa. An tattaro cewa akalla matasa 12 yan sandan suka kama wadanda sun kanannade gashin kansu.

Yanzu Yanzu: An kama jami’an yan sanda 3 akan mumunan harbi a Lagas
Yanzu Yanzu: An kama jami’an yan sanda 3 akan mumunan harbi a Lagas
Asali: Depositphotos

Sai wani zanga-zanga ya barke a kusa da wurin da abun ya faru, sannan a take abun ya karade yanar gizo inda kisan da aka yiwa Mista Johnson ya zama abun tattaunawa a shafukan zumunta.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ta gargadi Malami akan zaben Rivers

Wata majiya daga hukumar yan sanda ta bayyana cewa an kama jami’ai uku bisa umurnin Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu.

Shugaban yan sandan yace akwai yiwuwar jami’an da ke da hannu a rigimar na iya kasancewa sama da uku.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel