Shugabannin jam'iyyar PDP 'yan yunwa ne - Obasanjo

Shugabannin jam'iyyar PDP 'yan yunwa ne - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce ma fi yawa daga cikin shugabannin jam'iyyar PDP sun damu ne kawai da aljihunsu da cikinsu.

Da yake magana a yau, Litinin, yayin karbar bakuncin shugabannin jam'iyyar na yankin kudu maso yamma a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Obasanjo ya shawarci PDP da ta fitar da balagurbi daga cikinta.

Ya bayyana cewar balagurbi daga cikin mambobin jam'iyyar ne su ke hana ta samun nasara.

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa akwai bukatar hamayya mai karfin gaske domin gina siyasa mai inganci.

Obasanjo ya bukaci mambobin jam'iyyar adawa da su kara zage dantse tare da daukan matakan da zasu ceci siyasar kasa.

Shugabannin jam'iyyar PDP 'yan yunwa ne - Obasanjo
Obasanjo
Asali: UGC

Ya ce a shirye yake koda yaushe ya bayar da goyon baya ga duk wata kungiya ko jam'iyya da ke da kishin kasa.

"Na san cewar PDP zata fadi zabe a shekarar 2015, a bayyane ta ke, kuma na san akwai bukatar a sake fasalin jam'iyyar bayan ta fadi zabe.

"Akwai bukatar jaruman mutane da zasu iya jure dukan ruwa da zafin rana domin gina kasa a cikin jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Rikicin APC a Zamfara: Gwamna Yari ya yiwa Allah laifi - Sanata Marafa

"Zaka ga mutane masu kamala a fuska amma ba ka san mene ne a zuciyar su ba. Ku cire duk wanda ku ka fahinci cewar balagurbi ne, amma idan sun gyara halinsu sai ku sake basu dama.

"Ba zaka zama abokina a siyasa ba matukar baka da kishin Najeriya a zuciya. Har na bar duniya, zan cigaba da gwagwarmayar neman inganta Najeriya ne," a cewar Obasanjo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel