Zaben Zamfara: Ba mu da ta cewa sai dai mu bi umurnin Kotu - INEC

Zaben Zamfara: Ba mu da ta cewa sai dai mu bi umurnin Kotu - INEC

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta ce za ta ci gaba da kirdadon hukuncin kotun koli gabanin ta dauki mataki akan zaben fidda gwanayen takara na jam'iyyar APC a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar INEC na ci gaba da rike takardar shaidar cin zabe ta zababben gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Mukhtar Shehu, biyo bayan hukuncin da kotun koli ta zartar a birnin Shehu.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Asali: Twitter

A ranar Litinin kwamishinan hukumar INEC na sadarwa da yada rahotanni, Festus Okoye, ya ce hukumar na ci gaba da da'a ga umurnin kotu biyo bayan wasikar da jam'iyyar APC ta aike ma ta da ita na cewar kotu ba ta soke zaben fidda gwanayen takara da ta gudanar ba a jihar Zamfara.

A yayin kore shakku, hukumar INEC ta ba bu abin da ya shalle ta dangane da wanda ya kasance gwamnan jihar Zamfara illa iyaka za ta sauke nauyin da rataya wuyanta na bibiyar dokoki da kuma tsare-tsare a bisa adalci da gaskiya.

KARANTA KUMA: Hukumar NDLEA ta cafke masu fataucin kwayoyi 280 a jihar Kano

A yayin kyautata zato kan hukuncin da kotun koli za ta aiwatar, hukumar INEC ta ce akwai hakki na cancantar al'ummar jihar Zamfara su san kowa ne zai rike akalar su ta jagoranci domin gudanar da al'amurra na tsawon shekaru hudu masu gabatowa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel