Kiyasi: Tsawon rayuwar al'ummar Najeriya ba ya wuce shekaru 52 a doron kasa - Hukumar Kidaya

Kiyasi: Tsawon rayuwar al'ummar Najeriya ba ya wuce shekaru 52 a doron kasa - Hukumar Kidaya

Hukumar kidayar al'umma ta Najeriya NPC, National Population Commission, ta ce a halin yanzu tsawon rayuwa da al'ummar Najeriya ke shafewa a doron kasa ba ya wuce shekaru 52.2.

Mukaddashin shugaban hukumar, Hassan Bashir, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin gabatar da jawaban Najeriya a taron hadin gwiwar hukumomin kidaya na duniya karo na hamsin da biyu da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka.

Kamar yadda cibiyar lafiya ta duniya WHO ta bayyana, tsawon rayuwa da a turance ake kiran sa Life Expectancy, shi ne adadin lokaci da ake sa ran kowane jariri da aka haifi zai shafe a doron kasa a bisa la'aari na yawaitar mace-mace na wannan zamani.

Al'umma a Najeriya
Al'umma a Najeriya
Asali: Depositphotos

A yayin da a halin yanzu akwai kimanin al'umma fiye da miliyan 198 a fadin Najeriya, Mista Bashir ya ce kasa da kaso biyar ne cikin dari kacal suka haura shekaru 60 da haihuwa.

Haihuwar 'ya'ya na kan ma'auni na kaso 5.5 ga kowace Mace inda kaso 63 na al'ummar suka kasance kasa da shekaru 25 yayin da kaso 42 suka kasance kasa da shekaru 15 a ban kasa.

Binciken da hukumar NPC ta gudanar a kwana-kwanan nan cikin shekarar da ta gabata ya tabbatar da cewa, an samu juna biyu da ba bu shiri ko kuma niyya musamman cikin kaso 23 a tsakanin 'yan Mata masu shekarun 15 zuwa 19.

KARANTA KUMA: Ina fargabar abin da zai kasance da jam'iyyar APC a 2023 - Okorocha

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari ya sanya Mata da dama ke rasa rayukan su yayin haihuwa inda ake samun mace-mace 578 cikin kowace haihuwa 100,000.

Jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya, Tijjani Bande, yayin gabatar da na sa jawaban a madadin nahiyyar Afirka baki daya ya yi kira na neman a gaggauta samar da wasu tsare-tsare na domin tunkarar lamari na yawaitar adadin al'umma a yankin.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel