Hukumar NDLEA ta cafke masu fataucin kwayoyi 280 a jihar Kano

Hukumar NDLEA ta cafke masu fataucin kwayoyi 280 a jihar Kano

Hukumar hana ta'ammali da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, National Dr*gs Law Enforcement Agency, ta cika hannu da miyagu 280 masu safarar miyagun kwayoyi a fadin jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kwamandan hukumar na jihar, Dakta Ibrahim Abdul, shi ne ya bayar da shaidar hakan a ranar Litinin ya yi ganawa da manema labarai dangane da al'amurran da suka shafi yaki da ta'ammalin miyagun kwayoyi a watan Maris.

Hukumar NDLEA ta cafke masu fataucin kwayoyi 280 a jihar Kano
Hukumar NDLEA ta cafke masu fataucin kwayoyi 280 a jihar Kano
Asali: UGC

A cewar sa, hukumar ta samu nasarar cafke 'yan hana ruwa gudu a jihar Kano tun yayin da ta kaddamar shirin ta mai taken Sharar Miyagu domin kawo karshen ta'ammali da miyagun kwayoyi a Kanon Dabo.

Ya yi karin haske da cewar hukumar yayin cika hannun ta da miyagu ta kuma samu nasarar cafke miyagun kwayoyi da suka kai nauyin kilo 1,248.775 na nau'ika daban-daban da suka hadar da taba wiwi da kuma kwayoyin magani masu sanya maye da gushewar hankali.

KARANTA KUMA: Ka cire tallafin man fetur domin ci gaban Najeriya - BudgIT ta shawarci Buhari

A yayin da hukumar ta cika hannun ta da miyagu musamman a yankunan Tudun Wada, Kofar Nasarawa, Sabuwar Kofa da kuma Gandun Albasa dda ke kwaryar birnin Kano, Dakta Abdul ya kuma bayyana cewa, hukumar ta samu nasarar cafke hodar ibilis mai nauyin giram 52.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel