Ina fargabar abin da zai kasance da jam'iyyar APC a 2023 - Okorocha

Ina fargabar abin da zai kasance da jam'iyyar APC a 2023 - Okorocha

A ranar Litinin gwamnan jihar Imo Mista Rochas Okorocha, ya yi fargaba tare da gargadi na yiwuwar jam'iyyar APC mai ci za ta daidaice a zaben 2023 duba da irin rikon sakainar kashi ta jagoranta, Kwamared Adams Oshiomhole.

Gwamna Rochas ya kausasa harshe na dora laifi akan shugaban jam'iyyar su da cewar mummunar rawar da ya ke ci gaba da takawa a bisa kujerar jagoranci ita ce ummul aba isin da ta sanya jam'iyyar APC ta sha kaye a wasu jihohin inda ta gaza rike kujerun ta yayin zaben kasa.

Ina fargabar abin da zai kasance da jam'iyyar APC a 2023 - Okorocha
Ina fargabar abin da zai kasance da jam'iyyar APC a 2023 - Okorocha
Asali: Facebook

Mista Okoracha wanda a halin yanzu ya ke ci gaba da fafutikar samun takardar shaidar cin zaben Sanatan shiyyar Imo ta Tsakiya a hannun hukumar zabe INEC, ya yi furucin haka yayin wata hira da manema labarai bayan ganawar sa ta sirrance da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya yi tsokaci dangane da yadda jam'iyyar APC ke gudanar da al'amurranta na samar da shugabanni a sabuwar Majalisar tarayya, inda ya yi ikirarin cewa jam'iyyar ta mai she da yankin Kudu maso Gabashin kasar nan tamkar saniyar ware.

KARANTA KUMA: Ka cire tallafin man fetur domin ci gaban Najeriya - BudgIT ta shawarci Buhari

Okoracha ya ce nuna wariya ga yankin Kudu maso Gabas na daya daga cikin dalilai da za su jefa rudani a jam'iyyar APC da hakan zai yi tasirin gaske wajen kifewar ta yayin babban zaben kasa na 2023.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamna Okorocha ya ziyarci fadar shugaban kasa domin neman aminci da kuma gayyatar shugaban kasa Buhari wajen kaddamar da wasu muhimman ayyuka da ya kammala a jihar sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel