Bayan ganawa da shugaba Buhari, Okorocha ya fara hangen samun takardar shaidar cin zabe ta hukumar INEC

Bayan ganawa da shugaba Buhari, Okorocha ya fara hangen samun takardar shaidar cin zabe ta hukumar INEC

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya kasance a halin sauraron zuwan alheri da kyautata zato na samun takardar shaidar cin zabe ta hukumar zabe ta kasa INEC a matsayin zababben Sanatan shiyyar Imo ta Kudu.

Okorocha ya bayyana halin sauraron zuwan alheri yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawar sa ta sirrance tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin fadar Villa da ke garin Abuja a ranar Litinin.

Shugaba Buhari tare da Gwamna Okorocha

Shugaba Buhari tare da Gwamna Okorocha
Source: Facebook

Hukumar INEC na ci gaba da rikon takardar shaidar nasarar cin zabe ta gwamna Rochas a matsayin sa na zababben Sanatan Shiyyar Imo ta Kudu, a sakamakon zargin sa da tursasawa baturen zabe na jihar bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Tuni dai Okoracha ya shigar da koken sa gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja tare da rokon ta akan tilastawa hukumar INEC ta mallaka ma sa takardar shaidar cin zabe da ya ke ci gaba da ikirarin samun nasara.

Sai dai Okorocha ya fayyace dalilai na kai ziyarar sa zuwa fadar shugaban kasa da suka hadar da neman amincewa da kuma gayyatar shugaba Buhari wajen kaddamar da wasu muhimman ayyuka da ya gudanar a jihar sa.

KARANTA KUMA: INEC ta fara shirin rage adadin jam'iyyun siyasa na Najeriya

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Gwamna Rochas ta kammala wasu muhimman ayyuka na ci gaba da suka hadar da sabuwar tashar jirgin sama, babban ofishin 'yan sanda da kuma sabon babban ofishi na gidan yari.

A yayin da ta aiwatar da wannan muhimman ayyuka suka rataya a wuyan gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Imo ta dauki nauyin kammala su da suka hadar har da wasu sabbin cibiyoyin shari'a na kotun Justice Oputa da kuma babbar kotun jihar Imo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel