Jam’iyyar PDP ta gargadi Malami akan zaben Rivers

Jam’iyyar PDP ta gargadi Malami akan zaben Rivers

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta gargadi ministan shari’a, Abubakar Malami, bisa yunkurin hargitsa gudanarwar kiduddugan kuri’un zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a jihar Rivers.

Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) ta dakatar da tattara sakamakon zabe saboda rikici da ya mamaye zaben.

Hukumar ta kafa ranar 2 zuwa 5 ga watan Afrilu don cigaba da kidudduga don bayyana wanda ya lashe zaben.

A wani jawabin da kakakin PDP Kola Ologbondiyan ya gabatar jiya, yace dole Malami ya tsare kansa kuma kada ya yarda ayi amfani da shi wajen gudanar da ayyukan da suka saba ma doka a harkar da ya shafi zaben Rivers.

Jam’iyyar PDP ta gargadi Malami akan zaben Rivers
Jam’iyyar PDP ta gargadi Malami akan zaben Rivers
Asali: Depositphotos

Jam’iyyan ta kara gargadin Malami bisa zargin jawabin da ministan sufuri, Rotimi Amaeci yayi, cewa Malami na aiki don baiwa shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu umurnin, tsayar da tattara sakamakon.

KU KARANTA KUMA: Tambuwal ya roki shugabannin APC da su bashi goyon baya

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa anatan jihar Zamfara ta tsakiya, Kabiru Marafa, ya bayyana cewar gwamna Abdulaziz Yari na jihar ta Zamfara ya saba wa Allah a kan hakikicewar da yake yi a kan cewar jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fidda 'yan takara a Zamfara.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a kan harkokin siyasa a jihar Zamfara, Sanata Marafa ya bayyana cewar kamata ya yi gwamna Yari ya nemi yafiyar Allah a kan yaudarar da ya yiwa mutanen jihar Zamafara a kan batun zaben fidda 'yan takara.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel