Takarar shugabancin majalisa: Ndume bai janye wa Lawan ba - Kungiya

Takarar shugabancin majalisa: Ndume bai janye wa Lawan ba - Kungiya

- Wata kungiyar masu ruwa da tsaki musanta jita-jitan da ake yadawa na cewa Ndume ya janye daga takarar shugabancin majalisar dattawa

- Kakakin kungiyar, Samaila Ville ya ce labarin tsantsagwaron karya ce kuma ya bukaci al'umma suyi watsi da shi

- Ville ya ce Sanata Ndume ba zai taba janye wa daga takararsa ba sai ya tuntubi masu ruwa da tsaki a jihar Borno

Wata kungiyar masu ruwa da tsaki a kan siyasa a Borno ta karyata labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Sanata Ali Ndume da Danjuma Goje sun janye daga takarar shugabancin majalisar dattawa bayan ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari.

Wakilin Legit.ng daga Borno, Ndahi Inusa ya ruwaito cewa labarin na janyewar 'yan majalisar da ya yada a kafafen sada zumunta ya janyo hankulan al'umma sosai musamman a jihar Borno inda Ndume ya fito daga.

Takarar shugabancin majalisa: Ndume bai janye wa Lawan ba - Kungiya
Takarar shugabancin majalisa: Ndume bai janye wa Lawan ba - Kungiya
Asali: Facebook

A yayin da ya ke tsokaci a kan lamarin, shugaban kungiyar wasu mazauna Borno, Samaila Ville ya shaidawa wasu zababun 'yan jarida a Maiduguri cewa labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta ba gaskiya bane.

Ya ce ya yi mamakin ganin rubutu a kafar sada zumunta da ke cewa "Dan mu, Sanata Ndume ya janye daga takarar shugabancin majalisar dattawa bashin shi da tsohon gwamnan Gombe, Danjuma Goje sun gana da shugaban kasa.

"Duk da ya ke ba mu amince da labarin ba. Mun tuntubi Sanata Ndume kuma ya tabbatar mana labarin karya ne. Ya ce bai taba tunanin janye wa daga takarar ba."

Ya ce ba laifi bane idan Ndume yana bukatar a bawa kowa daman yin takarar kuma idan ma ana son bawa yankin Arewa maso gabas ne ya dace a bawa kowa damar shiga takarar.

"Mun kuma yi murnar jin cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole yana cewa ba zai zabi shugaban majalisar da karfi da yaji ba. Muna fata zai bari demokradiya tayi halinta a bari duk wanda ya lashe zaben ya zama shugaban majalisa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel