Siyasar Majalisa: Ibo su kuka da kan su inji Jam’iyyar APC

Siyasar Majalisa: Ibo su kuka da kan su inji Jam’iyyar APC

- Wani babba a cikin Jam’iyyar APC yace Mutanen Ibo ne su kayi wa kan su bakin-ciki a Majalisa

- APC tace ka da a ga laifin ta wajen raba kason kujerun da aka yi a Majalisar Tarayya wannan karo

Siyasar Majalisa: Ibo su kuka da kan su inji Jam’iyyar APC
Yekini Nabena yace Jam’iyyar APC ba ta samu kasuwa a Kudu ba
Asali: Twitter

Labari ya zo mana cewa Kakakin jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana cewa babu laifin APC don Ibo sun rasa samun manyan mukamai a majalisa. Yekini Nabena yace ka da a ga laifin APC wajen tsarin da ta dauka na kasa kujeru a majalisa.

Yekini Nabena yake cewa laifin Mutanen Yankin Kudu maso Gabas ne na kin marawa APC baya a zaben 2019 ya jawo aka maida ‘Yan majalisan da su ka fito daga shiyyar saniyar warewa wajen rabon mukamai masu tsoka a majalisar kasar.

Mista Nabena yana maida martani ne game da kukan da sabon Sanatan APC Orji Uzor-Kalu yake yi na cewa zai yi takarar shugaban majalisar dattawa idan har APC ta hana sa kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawan da yake hari.

KU KARANTA: Jagoran APC ya roki Sanata Ndume da Kalu su hakura da takara

Nabena yace jama’an Kudu ta Gabas sun marawa Atiku Abubakar baya ne a zaben da ya gabata don haka babu laifi don APC ta kebe ‘Yan majalisar da su ka fito daga wannan shiyya wajen zakulo wadanda za su rike shugaban majalisar kasar.

Kakakin na APC ya fadawa Orji Kalu cewa ya daina zargin kowa da hana sa takara illa mutanen sa da su ka fito kwan su da kwarkatar su, su ka zabi PDP a maimakon shugaba Buhari. Nabena yace kashi 90% na Ibo sun zabi Atiku ne a 2019.

A cewar Nabena, babu wanda zai taimakawa irin su Kalu a zaben majalisa tun da Atiku Abubakar ya sha kasa a zaben na bana. Haka kuma Nabena ya fadawa Kalu cewa babu wanda ya hana sa takara, amma ya san cewa ba zai kai ko ina ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel