Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga a jihar Zamfara, sun kubutar da mutanen da aka sace

Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga a jihar Zamfara, sun kubutar da mutanen da aka sace

Tawagar rundunar sojin saman Najeriya na mussamman da ke aiki a jihar Zamfara sun yi nasarar dakile wasu hare-haren yan bindigan da suka yi yunkurin kaib mamaya kauyukan Hayin Mahe da Hain Kanaa da ke karamar hukumar Gusau.

An gudanar da aikin kakkaban wanda ya gudana a jiya Lahadi, 31 ga watan Maris, biyo bayan samun rahoton da ke nuna cewa yan bangan, wadanda ke aiki a dajin Sububu da Kagara, sun kai hari kauyukan sannan suka sace wasu mutane.

Hakan yayi sanadiyar musayar wwuta a tsakaninsu da yan bangan inda rundunar sojin suka yi nasarar fatattaka yan fashin zuwa daji, sannan suka kashe mutum biyar, yayinda sauran suka tsere da harbin bindiga.

Anyi nasarar kwato mujallar bindigar AK-47 guda uku. Anyi nasarar ceto wasu mazauna kauyen, harda mata biyu da wani yaro da yan bindigar suka sace, an kuma mikasu ga sarkin garin Mada.

KU KARANTA KUMA: Dangane takardar shaidar cin zabe: Okorocha ya shiga ganawar sirri da Buhari

Bayan dakile harin, sojojin sun koma kauyukan domin ba mazauna yankin tabbacin tsaron lafiyar su da dukiyoyi da kuma tabbatar da cewar 'yan bindigar ba su dawo domin daukar fansa ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel