Ranar kin dillanci: Kotu ta dauki tsatstsauran mataki kan mai yi ma matan aure fyade

Ranar kin dillanci: Kotu ta dauki tsatstsauran mataki kan mai yi ma matan aure fyade

Wata karamar kotun majistri dake garin Ebute Meta ta jahar Legas ta bada umarnin garkame wani mutumi mai suna Abiodun Ibraheem a gidan kurkuku sakamakon zarginsa da ake yi da yi ma matar aure fyade.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu ne Alkalin kotun, mai sharia O.R Williams Isichie ce ta yanke wannan hukunci, inda ta bukaci a daureshi har zuwa ranar 2 ga watan Mayun 2019.

KU KARANTA: Zaben Kano: Shugaba Buhari bai ji dadin abubuwan da suka faru ba

Ana karar Ibraheem a gaban kotun ne akan tuhume tuhume guda uku da suka shafi fyade, hadin baki da kuma satar mutu, haka nan duk magiyar da yayi ma kotun tare da neman sassauci bai amsu a wajen Alkali Williams ba.

Da farkon zaman, Dansanda mai shigar da kara, Inpekta Maria Dauda ta shaida ma kotun cewa Ibraheem mai shekaru 35 tare da wasu mutane a da yanzu suka tsere, sun aikata laifin ne a ranar 25 ga watan Maris, a gida mai lamba 77, Bola street, Ebute Meta.

Yarsanda Maria tace da karfi da yaji mutanen suka yi ma matar auren da ba’a bayyana sunanta ba fyade, daga nan kuma suka saceta tare da danta guda daya, inda tace laifin ya saba ma sashi na 260, 268 da 411 na kundin hukunta manyan laifuka.

Daga karshe bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkalin kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Mayu, sa’annan ta bukaci a mika karar zuwa ofishin babban jami’in shigar da kara ta jahar Legas domin samun shawara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel