Zan yi wa yan Najeriya iya bakin kokarina a karo na biyu - Buhari

Zan yi wa yan Najeriya iya bakin kokarina a karo na biyu - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu a Abuja ya ba da tabbacin cewa zai yi iya bakin kokarinsa don tabbatar da ci gaban yan Najeriya a mulkinsa na biyu wanda za a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari ya yi jinjina tare da yaba wa wadanda suka zabe shi a lokacin zabe.

Buhari yayi maganan ne yayinda ya karbi bakuncin kungiyar ci gaban Jihar Katsina wanda justice Mamman Nasir ya jagoranta a fadar shugaban kasa, Abuja.

Shugaban kasar ya bayyana cewa yawan jam’an da suka tarbi jirgin yakin neman zaben shi a kowace jiha ya wuci tsammanin kowa, yayin da yake danganta yawan jama’an da kokarin da gwamnatinsa tayi.

Zan yi wa yan Najeriya iya bakin kokarina a karo na na biyu - Buhari
Zan yi wa yan Najeriya iya bakin kokarina a karo na na biyu - Buhari
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa ya riki mukamin shugaban kungiyar ci gaban jihar Katsina har na tsawon shekaru 17, wanda a wannan lokacin ne ya gudanar da yawancin ayyuka don goyon baya ga fannin ilimi, kiwon lafiya da harkan noma a jihan, musamman ga mabukatu.

KU KARANTA KUMA: Tambuwal ya roki shugabannin APC da su bashi goyon baya

Yayinda yake nuna ra’ayinsa, Galadiman Katsina, Justice Nasiru, yace kungiyar na mika godiya ga Allah da kuma yan Najeriya akan damar da suka baiwa shugaban kasa Buhari a karo na biyu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel