Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara

Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara

Rundunar sojin sama ta bayyana cewar ta kashe a kalla 'yan bindiga biyar bayan ta dakile wani hari da su ka yi yunkurin kai wa wasu kauyuka da ke karkashin karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

A cikin wani jawabi da ta fitar a yau, Litinin, ta bakin Ibikunle Daramola, darektan yada labarai da hulda da jama'a, NAF ta ce wasu daga cikin 'yan bindigar sun tsere da ciwukan harbin bindiga bayan musayar wuta.

Ya bayyana cewar dakarun soji sun yi nasarar kubutar da wani karamin yaro da wasu mata biyu da 'yan bindigar su ka yi garkuwa da su.

Daramola ya ce, "rundunar sojin sama ta musamman (SF) da ke aiki a jihar Zamfara ta dakile wani hari da 'yan bindiga su ka kai kauyukan Hayin Mahe da Hayin Kanawa da ke karkashin karamar hukumar Gusau.

Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara
Wasu jama'ar jihar Zamfara a layin karbar asirin tsare kai
Asali: Twitter

"Jami'an mu sun yi nasarar dakile harin da 'yan bindigar su ka yi yunkurin kai wa a ranar 31 ga watan Maris bayan samun bayanan sirri da su ka tabbatar da cewar wasu 'yan bindiga daga dajin Sububu da Kagara na shirin kai hare-hare tare da sace mutane domin yin garkuwa da su.

"Dakarun mu sun mayar da martani a kan lokaci, lamarin ya haifar da musayar wuta a tsakani kafin daga bisani 'yan bindigar su ruga zuwa cikin daji. Amma duk da haka sai da jami'an mu su ka bi su har cikin dajin inda su ka kashe biyar daga cikin su, yayin da wasu daga cikinsu su ka tsere da raunuka sakamakon harbin bindiga.

DUBA WANNAN: Abinda aka yiwa masu garkuwa da mutane kafin su sake ni - Sheikh Sulaiman

"Mun samu bindigu samfurin Ak-47 guda uku, sannan mun kubutar da wasu mata biyu da wani karamin yaro guda da 'yan bindigar su ka sace daga kauyukan domin yin garkuwa da su,tuni mun mika su ga hakimin garin Mada.

"Bayan dakile harin, dakarun soji sun koma kauyukan domin bawa jama'a tabbacin tsaron lafiyar su da dukiyoyi da kuma tabbatar da cewar 'yan bindigar ba su dawo domin daukan fansa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel