Tambuwal ya roki shugabannin APC da su bashi goyon baya

Tambuwal ya roki shugabannin APC da su bashi goyon baya

Gwwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya bukaci shugabannin jam’ iyyar All Progressives Congress (APC), da magoya bayansu da su hada hannu da gwamnatinsa dmin ci gaban jihar.

A wani jwwabi daga babban hadiminsa akan ayyuka na mussamman, Yusuf Dingiadi, a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris a Kaduna, Tambuwal ya bayyana cewa zaben gwamna da na majalisar dokokin jihar da aka yi ya wuce, yanzu lokaci ne na ci gaban jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta bayyana cewa bayan zaben da aka sake a yankunan jihar, INEC ta kaddamar da Gwamna Tambuwal na PDP, a matsayin wanda ya lashe zabe da tazara 341.

Tambuwal ya roki shugabannin APC da su bashi goyon baya
Tambuwal ya roki shugabannin APC da su bashi goyon baya
Asali: Twitter

Tambuwal ya samu kuri’u 512,002, yayinda babban abokin adawarsa, Ahmed Aliyu na APC kuri’u 511,661 a tseren gwamna.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Mutanen Borno na tare da Ndume – Jigon APC

Ya bukaci fusatattun jam’iyyun siyasa da kada su tayar da rikici, maimakon haka su tunkari kotun zabe kamar yadda doka ta tanadar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kan ganawa da gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Okorocha wanda jam'iyyar APC ta dakatar da shi akan zarginsa da yiwa jam'iyya zagon kasa, ya isa fadar shugaban kasar da misalin karfe 1 na rana inda kuma kai tsaye ya shiga ofishin shugaban kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel