Takardar cin zabe: INEC ba ta so na zama shugaban majalisar dattijai - Uwajumogu

Takardar cin zabe: INEC ba ta so na zama shugaban majalisar dattijai - Uwajumogu

- Sanata Benjamin Uwajumogu ya koka kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta hana shi takardar shaidar cin zabe

- Uwajumoga ya ce hana shi takardar shaidar cin zaben zai hana shi cimma kudurinsa na tsayawa takarar kujerar shugaban majalisar dattijai ta 9

- Yana mai cewa hukumar zaben ta dogara ne kawai da wata dokar kotu ta hana shi takardar cin zaben bayan da wani dan takarar kujerar ya shigar da kara

Sanata mai wakilatar mazabar shiyyar Okigwe, Benjamin Uwajumogu, wanda kuma shi ne dan takarar jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a zaben ranar 23 ga watan Fabreru, ya koka kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta hana shi takardar shaidar cin zabe.

Uwajumoga ya ce hana shi takardar shaidar cin zaben zai hana shi cimma kudurinsa na tsayawa takarar kujerar shugaban majalisar dattijai ta 9.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana zaben mazabar Imo ta Arewa (shiyyar Okigwe) a matsayin zaben da bai kammala ba.

Wannan kuwa na zuwa kwanaki hudu bayan da wasu da ba a san ko su waye ba suka cinnawa ofishin INEC da ke karamar hukumar Isiala a mazabar wuta.

KARANTA WANNAN: Dangane takardar shaidar cin zabe: Okorocha ya shiga ganawar sirri da Buhari

Takardar cin zabe: INEC ba ta so na zama shugaban majalisar dattijai - Uwajumogu
Takardar cin zabe: INEC ba ta so na zama shugaban majalisar dattijai - Uwajumogu
Asali: Getty Images

Sai dai Uwajumogu a zantawarsa da manema labarai a Isiala Mbano bayan halartar wani taron karramawa da lambar girma ta 'ICON of CWO' da kungiyar matan Katolika ta St Michael Catholic, Umueze ta yiwa Chief Tony Chukwu, ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben.

Ya ce an gudanar da zaben lami lafiya kuma an tattara sakamakon zaben kamar yadda INEC ta tanadar, yana mai cewa hukumar zaben ta dogara ne kawai da wata dokar kotu ta hana shi takardar cin zaben bayan da wani dan takarar kujerar ya shigar da kara.

Ya ce: "Bai kamata ace an bayyana zaben a matsayin zaben da bai kammala ba saboda an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali kuma an sanar da sakamako. Matsalar kawai ita ce mutum daya ya shigar da kara kotu kuma ina tunanin cewa bai kamata INEC ta hana ni takardar cin zabe ba, domin ba ta da wani dalili."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel