Dangane takardar shaidar cin zabe: Okorocha ya shiga ganawar sirri da Buhari

Dangane takardar shaidar cin zabe: Okorocha ya shiga ganawar sirri da Buhari

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kan ganawa da gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Okorocha wanda jam'iyyar APC ta dakatar da shi akan zarginsa da yiwa jam'iyya zagon kasa, ya isa fadar shugaban kasar da misalin karfe 1 na rana inda kuma kai tsaye ya shiga ofishin shugaban kasar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Muna tsumayin Buhari ya kawo sunan wanda zai maye gurbin Magu - Saraki

Gwamnan, wanda kuma shi ne zababben sanatan mazabar Imo ta Yamma na fuskantar kalubale daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC akan hana shi takardar shaidar cin zabe.

Hukumar dai har yanzu ba ta bashi takardar shaidar cin zabe ba.

Cikakken lamarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel