Da duminsa: Muna tsumayin Buhari ya kawo sunan wanda zai maye gurbin Magu - Saraki

Da duminsa: Muna tsumayin Buhari ya kawo sunan wanda zai maye gurbin Magu - Saraki

- Bukola Saraki ya ce har yanzu hukumar EFCC ba ta da wani tsayayyen shugaba saboda gwamnatin Buhari ta gaza maye gurbin Mr. Ibrahim Magu

- Ya ce ya zama wajibi gwamnatin Buhari ta sake gabatar da sunan wani ko kuma ta bi hanyar zagaye shuwagabannin majalisar dattijan a siyasance

- Saraki ya shaidawa zababbun 'yan majalisar da su sani cewa suna da karfin ikon tabbatarwa ko kuma kin tabbatar da sunayen da shugaban kasa zai gabatar masu

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki ya ce har yanzu hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC ba ta da wani tsayayyen shugaba saboda gwamnatin Buhari ta gaza maye gurbin Mr. Ibrahim Magu, a lokacin da majalisar dattijai ta ki amincewa da sunansa.

Saraki ya bayyana hakan a lokacin wani buki da aka shirya na wayar da kan zababbun mambobin majalisar tarayya da za su shiga majalisar ta 9.

Ya ce ya zama wajibi gwamnatin Buhari ta bi matakan da suka dace na ko ta sake gabatar da sunan wani ko kuma ta bi hanyar zagaye shuwagabannin majalisar dattijan a siyasance.

KARANTA WANNAN: Majalisar tarayya ta 9: Gbajabiamila ya tsaya takarar kujerar kakakin majalisa

Da duminsa: Muna tsumayin Buhari ya kawo sunan wanda zai maye gurbin Magu - Saraki
Da duminsa: Muna tsumayin Buhari ya kawo sunan wanda zai maye gurbin Magu - Saraki
Asali: Facebook

Saraki ya shaidawa zababbun 'yan majalisar da su sani cewa majalisar dattijai na da karfin ikon tabbatarwa ko kuma kin tabbatar da sunayen da shugaban kasa zai gabatar masu akan nadin wani mukami.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa majalisar dattijai ta ki amincewa da bukatar fadar shugaban kasa na sanya Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC har sau ukku, bisa dogara da hujjar wani bayani da suka samu daga hukumar tsaro da DSS akansa.

Saraki ya yi nuni da cewa mumman kallon da jama'a suke yiwa majalisar tarayya ya sa har majalisar ta 8 ta yi bakin jini duk da cewa tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin doka.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel