Zaben Kano: Shugaba Buhari bai ji dadin abubuwan da suka faru ba

Zaben Kano: Shugaba Buhari bai ji dadin abubuwan da suka faru ba

Wata kungiyar matasan jam’iyyar APC mai suna All Progressive Youth Forum ta bayyana damuwarta game da abubuwan da suka faru yayin kammala zaben gwamnan jahar Kano, sa’annan ta wanke shugaban kasa Muhammadu Buhari daga zarginsa da ake yi da hannu cikin bahallatsar.

Shugaban kungiyar, Alwan Hassan ye bayyana ma majiyar Legit.ng haka inda yace tuni sun katabta wata dagouwar waraka, kuma sun aiketa ga shugaban jam’iyyar APC ta kasa, kwamared Adams Oshiomole.

KU KARANTA: Wata sabuwa inji yan caca: An baiwa dalibai lasisin shan sigari don fahimtar darasi

Zaben Kano: Shugaba Buhari bai ji dadin abubuwan da suka faru ba
Buhari da Ganduje
Asali: Depositphotos

Alwan yace sun dauki wannan mataki ne sakamakon ganin yadda kaunar da Kanawa ke yi ma Buhari ta ja baya ba don komai ba sai don irin bahallatsar da wasu jiga jigan APC suka tafka a yayin zaben, kuma jama’a ke ganin Buhari bai hanasu ba.

Kungiyar tace Buhari ya kame bakinsa daga yin magana ne domin kada a zargeshi da goyon bayan wani bangare, don haka ya sanya idanu don baiwa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, da rundunar Yansanda sun gudanar da ayyukansu.

“Wallahi tallahi Buhari bai ji dadin abinda ya faru a Kano ba, kuma baya tare da abinda ya faru a Kano, babu ruwan shugaban kasa a wannan harkar saboda ai tunda farko Buhari yace a zabi dan takarar gwamnan da jama’a suka san zai yi adalci.” Inji shi.

Daga karshe Alwan yayi kira ga uwar jam’iyyar APC ta gudanar da binciken kwakwaf don gano wadanda suka shigi da yan daba suka hana mutane fita zabe a yayin zaben Kano, sa’annan suka rubuta sakamako?

“Duk wanda aka kama da wannan laifi, tabbas kamata yayi jam’iyya ta sallameshi a matsayin hukuncinsa, muma muna da cikakken shaidu game da badakalar da wasu jiga jigan APC suka tafka a yayin zaben.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel