Shugabancin majalisar dattawa: Mutanen Borno na tare da Ndume – Jigon APC

Shugabancin majalisar dattawa: Mutanen Borno na tare da Ndume – Jigon APC

- Sanata Ali Ndume ya samu goyon baya daga jiharsa a kudurin shi na son zama shugaban majalisar dattawa

- Babban jagran kungiyar kamfen din Muhammadu Buhari/Osinbajo (MBO), Hon. Usman Ibrahim ne ya bayyana haka

-Ibrahim wanda ya kasance dan asalin yankin Born ta tsakiya ya bayyana cewa al’umman jihar Borno na bukatar Ndume ya zama shugaban majalisar dattawa

Jagoran kungiyar kamfen din Shugaban kasa Muhammadu Buhari/Osinbajo, Hon. Usman Ibrahim, ya bukaci Sanata Ali Ndume da kada ya janye daga takaran shugabancin majalisan dattawa.

A wani hira tare da jaridar Leadership a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris a Abuja, Ibrahim wanda ya fito daga yankin Borno ta tsakiya ya bayyana cewa al’umman Borno suna da bukatan Ndume ya zama shugaban majalisan dattawa.

Ibrahim ya bayyana cewa kungiyarsu za ta yi taro a Abuja don bayyana wa al’umma goyon bayanta ga kudirin Ndume, inda ya kara da cewa dan majalisar na bukatan ramuwar biyayya da yayi wa gwamnatin Buhari.

Shugabancin majalisar dattawa: Mutanen Borno na tare da Ndume – Jigon APC
Shugabancin majalisar dattawa: Mutanen Borno na tare da Ndume – Jigon APC
Asali: Facebook

Har ila yau, Sanata Suleiman Hunkuyi ya bayyana wa yan jarida a karshen makon da ya gabata cewa tsayar da dan takara guda daya a matsayin shugaban majalisa ba tsarin damokardiyya bane.

Ya bayyana cewa amincewa da hakan ba zai yi aiki ba saboda matsayin shugaban majalisa ko kakakin majalisa bai kasance da zabe ba ko da basu kasance mambobin majalisar ba.

KU KARANTA KUMA: Ayi umurnin sake sabon zabe ba tare da dan takarar APC ba – Shinkafi ga kotun zabe

A halin da ake ciki, kungiyar magoya bayan Buhari-Osinbajo a yankin Arewa maso Gabas sun tsayar da Sanata Ndume a matsayin wanda zai nemi shugaban majalisan dattawa.

Kungiyoyin sun ce suna da tabbacin cewa jagorancin Ndume a majalisan dattawa za ta hada kai majalisan zartarwa don cigaban Najeriya.

Kungiyar a wani jawabi wanda ke dauke da sa hannun mai gudanarwarta, Hon. Salisu Sabo yace magoya bayan kungiyar shugaban kasa Mihammadu Buhari da masu ruwa da tsaki a APC daga jihohi shida dake yankin Arewa maso Gabas ma sun mara wa Sanata Ndume baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel