Za mu hukunta wadanda suka haddasa faduwar Buhari a Anambra - APC

Za mu hukunta wadanda suka haddasa faduwar Buhari a Anambra - APC

- Jam’iyyar APC ta kafa wani kwamiti domin bincikar faduwarta a jihar Anambra a lokacin zaben Shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu

- Jam'iyyar tace adadin kuri’un da ta samu a jihar bai yi daidai da tsayuwar siyasar jam’iyyar a jihar ba

- APC ta kuma sha alwashin hukunta duk wanda ta samu da hannu a faduwarta

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kafa wani kwamiti domin bincikar faduwarta a jihar Anambra a lokacin zaben Shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu.

A cewar jam’iyyar, adadin kuri’un da jam’ iyyar ta samu a jihar bai yi daidai da tsayuwar siyasar jam’iyyar a jihar ba.

Za mu hukunta wadanda suka haddasa faduwar Buhari a Anambra - APC
Za mu hukunta wadanda suka haddasa faduwar Buhari a Anambra - APC
Asali: Twitter

Asil Ejidike, mukaddashin Shugaban jam’iyyar a jihar, ya rantsar da kwamitin mutum 13 a sakatariyar jam’iyyar da ke Awka, babbar birnin jihar Anambra a karshen mako, jaridar Punch ta ruwaito.

Da yake magana a wajen bikin kaddamar da kwamitin, yace: “ Mun tabbatar da shahararmu a jihar, mun yi mamakin cewa dan takararmu ya fadi zabe a jihar.

KU KARANTA KUMA: Ayi umurnin sake sabon zabe ba tare da dan takarar APC ba – Shinkafi ga kotun zabe

“Shine dalilin da yasa ya zama dole mu binciki dalilan da suka samu faduwa sannan mu hukunta mambobinmu da aka kama da hannu a faduwar.

“An kafa jam’iyyun siyasa ne dmin lashe zabe, sannan idan har ba za mu iya lashe zaben ba, toh bamu cikin harkar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel