Ayi umurnin sake sabon zabe ba tare da dan takarar APC ba – Shinkafi ga kotun zabe

Ayi umurnin sake sabon zabe ba tare da dan takarar APC ba – Shinkafi ga kotun zabe

Alhaji Sani Shinkafi, dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a zaben 2019 da aka yi a jihar Zamfara, yayi kira ga sake sabon zabe ba tare da yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba.

Shinkafi ya bukaci kotun zabe na gwamna da majalisar dokokin jihar da ke zaune a Abuja da ta soke zaben gwamnan da aka gudanar a jihar a ranar 9 ga watan Maris, sannan tayi umurni ga sake sabon zabe ba tare da APC da dan takararta Mukhtar Shehu Idris ba.

A wani korafi da ya shigar gaban kotun zaben a ranar 29 ga watan Maris, Shinkafi ta hannun lauyansa, Ifeanyi Mbaeri, yace sashi na 177(c) na kundin tsarin mulki na 1999 kamar yadda aka gyara ya nuna cewa "Mutum zai cancanci yin takarar kujerar Gwamnan jiha; idan ya kasance mamba a wata jam'iyyar siyasa sannan jam'iyyar siyasar ta dauki nauyin takararshi."

Ayi umurnin sake sabon zabe ba tare dad an takarar APC ba – Shinkafi ga kotun zabe
Ayi umurnin sake sabon zabe ba tare dad an takarar APC ba – Shinkafi ga kotun zabe
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Shikafi ya kuma bayyana cewa duk jam'iyyar siyasa da ke neman daukar nauyin wani dan takara ko tsayar da shi a karkashin wannan sashi ya zama dole ta gudanar da zaben fidda gwani wajen zabar dukkanin mukamanta.

KU KARANTA KUMA: Damokradiyyar kasar nan na fuskantar barazana - Musa Rabiu

Da yake nuni ga sashi na 140(2) na dokar zaben 2010 kamar yadda aka gyara, dan takarar na APGA yace: "A inda kotun zabe ko kotu ta soke wani zabe da aka riga aka yi kuma cewa dan takarar da ya samu kuri'u mafi yawa a zaben bai cancanci takara ba ko kuma ace kotu ba za ta kaddamar da wanda ya zo na biyu a matsayin wanda ya lashe zabe ba, toh sai a sake sabon zabe."

Ya kuma bukaci kotun zabe da ta yi umurni ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) akan ta sake gudanar da sabn zabe a jihar ba tare da sanya dan takarar jam'iyyar APC a cikin ba cikin kwanaki 90.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel