Rikicin Kaduna: An kashe mutane 148, lalata gidaje 545 a rikicin da yaki karewa

Rikicin Kaduna: An kashe mutane 148, lalata gidaje 545 a rikicin da yaki karewa

Al'umman garin Adara a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna sun bayyana cewa ana bukatar kimanin milyan hamsin domin sake gina gidaje 545 da yan bindiga suka lalata a hare-hare.

Shugaban al'ummar, Mumumi Madugu, ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai ranar Lahadi, a jihar Kaduna inda yace dubunnan al'ummarsa sun gudu daga muhallinsu.

Mista Madugu ya ce al'ummar ta fara fuskantar hare-hare ne bayan jawabin gwamnati jihar Kaduna ranar 15 ga watan Febrairu cewa an kashe wasu yan Fulani, matansu da yaransu akalla 60.

Ya ce hare-hare da aka kai tsakanin 10 ga Febrairu da 11 ga Maris, ya bar mutane a mace 148 da gidaje 545 a rushe.

KU KARANTA: Gwamnoni sun shige wa Lawan gaba a tseren shugaban majalisar dattawa

Yace: "Yan bindigan da yawansu sun kai hari Unguwan Barde inda suka kashe mutane 35 kuma suka lalata gidaje 90 sannan suka garzaya kauyen Karamai ranar 2 ga watan Febrairu inda suka kashe mutane 42 da rusa gidaje 196."

"A ranar 11 ga Maris, an kai hari garin Dogon Noma inda aka hallaka mutane 71, kuma aka rusa gidaje 259. A dukkan hare-haren, mutane 65 sun jikkata kuma an lalata kayan masarufin kimanin milyan 28."

"Wadannan hare-hare sun kori dubunnan mutane daga muhallansu, yara 2000 na rayuwa a sansanin gudun hijra dake Chikun, Kajuru da Kachia," Yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel