Damokradiyyar kasar nan na fuskantar barazana - Musa Rabiu

Damokradiyyar kasar nan na fuskantar barazana - Musa Rabiu

Wani shahararren dan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Musa Rabiu ya bayyana cewa damokradiyyar kasar nan na cikin hatsari duba ga yadda ake cece-kuce a zabukan kasar.

A cewarsa hakan na iya jefa damokradiyyar kasar a cikin wani irin hali na rashin tabbass, ta yadda al’ umma ba za su aminta da lamarin ba.

Dan kasuwar ya bayyana hakan ne a zantawa da yayi da manema labarai.

Ya kuma yi nuni ga cewa, zaben kasar na fuskantar wani sabon sal da ba a saba gani ba a lokutan baya, an fara samun rikici ne tun daga matakin zaben fidda gwanin kowace jam’ iyya. A wasu jam’iyyun ba a ma yi zaben fidda gwani ba, inda hakan ya sanya wasu kotuna sun fara rusa zabukan da aka yi a wasu jihohi.

Damokradiyyar kasar nan na fuskantar barazana - Musa Rabiu
Damokradiyyar kasar nan na fuskantar barazana - Musa Rabiu
Asali: UGC

Alhaji Musa Rabiu yace tsarin zaben da ake ba irin na baya bane da mutum sai ya fito yayi takara ya shiga zaben fidda gwani, idan akace anyi zaben fidda gwani sahihi baza kaji wani dan takara ya fita daga jam’iyya da yake ba ya koma wata saboda ya yarda da sahihancin zabe daya fito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni sun shige wa Lawan gaba a tseren shugaban majalisar dattawa

Amma yanzu da yake dauki dora ake sai wadansu su fita su koma wata dan neman takara wannan ya nuna ba zancen damokradiyya a tafiyar siyasar Najeriya a halin yanzu,shi yasa in anzo zaben gama gari ake dauki-dora saboda tun farko an rusa ginshikin Damokradiyyar.

Rabiu yaja hankalin Matasa da su ne akafi yin anfani dasu wajen cutarda cigabansu dana al’umma da cewa su gujewa duk wani da zai anfani da su don cimma mummunar wani abu na son ransa ta yayi anfani dasu ta basu kwayoyi. Maimakon haka su tsaya akan neman ilimi da sana’oi domin su zama masu gina kansu da ci gaban al’umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel