Gwamnoni sun shige wa Lawan gaba a tseren shugaban majalisar dattawa

Gwamnoni sun shige wa Lawan gaba a tseren shugaban majalisar dattawa

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun fara gwagwarmaya, domin shige wa Sanata Ahmad Lawan gaba wajen ganin ya zama Shugaban majalisar dattawa.

Wasu daga cikinsu sun gana a daren jiya, Lahadi a Abuja kan yadda za su karfafa ajandar Lawan. Shine zabin jam’iyyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lawan ya halarci taron, wanda ake ganin yana daga cikin matakan da masu ruwa da tsaki na APC ke bi gabannin rantsar da majalisar dokokin kasar na tara.

Taron wanda aka fara da misalin karfe 8pm, ya kai har karfe 10:30 na dare. Sai dai ba a bayyana jerin gwamnonin da sauran mutane da suka halarci tattaunawar ba.

Gwamnoni sun shige wa Lawan gaba a tseren shugaban majalisar dattawa
Gwamnoni sun shige wa Lawan gaba a tseren shugaban majalisar dattawa
Asali: UGC

An tattaro cewa a ranar Litinin da ya gabata bayan jam’iyyar ta lamuncewa Lawan, Shugaban kasar ya bukaci mambobin jam’iyyar da su “duba inganci wajen yiwayan Najeriya zabi, musamman zababbun sanatoci”.

Daya daga cikin wadanda suka shirya taron, ya bayyana cewa: “an sanar da ganawar ne bisa ga umurnin Shugaban kasa zuwa ga gwamnoni don ganin an isar da ajandar Lawan wajen ganin ci gaban kasar."

KU KARANTA KUMA: An shiga fargaba a majalisar dokokin Jigawa kan yunkurin tsige kakakin majalisa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na zuba ido don ganin Sanata Goje ya janye kudirinsa na tseren kujerar Shugaban majalisaer dattawa.

Ana sanya ran Goje (Gombe ta tsakiya), daya daga cikin yan takarar kujerar zai janyewa Dr. Ahmed Lawan, Shugaban masu rinjaye a majalisa wanda ke da cikakken goyon bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Shugaban kasa Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel