Najeriya ce kasa mafi takaici ta 6 a duniya - Binciken jami'ar John Hopkins

Najeriya ce kasa mafi takaici ta 6 a duniya - Binciken jami'ar John Hopkins

Sabuwar rahoton da Steve Hanke, masanin tattalin arziki daga jam'iyyar John Hopkins dake Amurka, ya lissafa Najeriya, Venezuela, Iran Brazil, cikin kasashe goma mafi takaicin zama a fadin duniya.

Game da rahoton, kasar Venezuela ce aka alanta a matsayin kasa mafi talauci, mafi takaici a fadin duniya. Hanke yace: "Kasar Venezuela ce ta kara zuwa na daya a matsayin kasa mafi takaici a duniya a 201 kamar yadda ta zo a 2017, 2016, da 2015.”

Najeriya ce kasa mafi takaici ta 6 a duniya - Binciken jami'ar John Hopkins
Najeriya ce kasa mafi takaici ta 6 a duniya - Binciken jami'ar John Hopkins
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kujerar Kakakin majalisa: Duk da zabin jam'iyya, mutane 8 za suyi takara

Kasar Argentina kuwa, ta dade tana fuskantar matsin tattalin arziki saboda irin badakala da ya cika kasar da rashin darajar kudin kasa. Kasar Iran ce ta zo na uku sannan kasar Brazil ta zo na hudu.

Bincike ya daura kasar Turkiyya matsayin kasa na biyar mai takaici, sannan gida Najeriya ta zo na shida. An gudanar da wannan lissafi ne bisa yawan rashin aikin yi, hauhawar farashi da kuma kudin ruwa.

A bangare guda, Ɗan takarar shugabancin ƙasar nan ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP Alhaji Sule Lamiɗo, ya bayyana cewa halin matsi da yunwa da kuma matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar nan duk jam'iyyar APC ce ƙarƙashin jagorancin shugaban Muhammadu Buhari ta kawo su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel